Sanatocin Najeriya sun umarci Buhari ya tsige kafatanin shuwagabannin hukumomin tsaro na Najeriya

Sanatocin Najeriya sun umarci Buhari ya tsige kafatanin shuwagabannin hukumomin tsaro na Najeriya

Sakamakon matsalolin tsaro daban daban da ake fuskanta a Najeriya, musamman a jihar Benuwe, inda lamarin ya gagari kundila, yan majalisar dattawa sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sallami kafatin shuwagabannin hukumomin tsaron Najeriya.

Jaridar The Nation ta ruwaito Sanatocin na fadin matsalar tsaro na cigaba da ta’azzara ne sakamakon sakacin shuwagabannin hukumomin tsaro da rashin kwarewa irin nasu, tare da bukatar gwamnati ta nemi taimako daga kasashen waje, idan har hakan zai kawo karshen matsalar.

KU KARANTA: Daukar dala ba gammo: Ka halasta Luwaɗi da maɗigo a Najeriya – Shugaban kasar Ingila ga Buhari

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sanatan jama’an Kudan Nassarawa, Sulaiman Adokwe ne ya janyo hankalin majalisar game da hare haren, inda yace har yanzu ana kashe kashe a mazabarsa a tsakanin mazauna kauyuka da makiyaya.

Sanatocin Najeriya sun umarci Buhari ya tsige kafatanin shuwagabannin hukumomin tsaro na Najeriya
Sanatocin Najeriya

Sanatan ya koka kan cewa zuwa yanzu makiyaya sun kashe muatne 70 a mazabarsa, inda yace da alama makiyayan sun yi nufin karar da yan kabila Tibi dake mazabarsa kenan;

“Makiyaya na cigaba da kai hare haren kisan kare a dangi a kudancin Nasarrawa, tun a karshen makon da ta gabata, yawancin wadanda suka kashe yan kabilar Tibi ne, sun jikkata wasu da dama, tare da fatattakar dubun dubatan jama’a daga gidanjensu.” Inji shi

Sanata Adokwe ya nuna mamakinsa game da yadda Sojoji da sauran jami’an hukumomin tsaro suka gagara shawo kan matsalar, duk da kwashe kwanaki hudu makiyaya na kai hare haren. Shi ma takwaransa, Barbanabas Gemade ya nuna damuwarsa ga hare haren.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng