Tsarabar juma'a: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da kabarin Annabi Muhammad SAW
Makwancin Annabi Muhammadu S. A. W ko shakka babu yana da matukar muhimmanci ga daukacin al'ummar musulmai inda dubun dubatar su ne ke ziyartar kabarin na sa a duk shekara dake a masallacin sa na Madina.
Ga dai wasu muhimman bayanai nan game da kabarin na fiyayyen halitta da ya kamata ku sani:
1. An zagaye makwancin na fiyayyen halittan ne tare da sauran khalifofin sa Abubakar da Umar da kwalliyar zinare a bagiren da ake cewa Raudah.
KU KARANTA: Jam'iyyar PDP ta jajantawa 'yan Shi'a
2. An rufe manzon Allah S. A. W din ne bayan wafatin sa a dakin matar sa kuma uwar muminai Aisha yaddar Allah ta tabbata a gare ta.
3. Akwai wasu 'yan kofofi guda uku a jere da juna dake yin ishara da kaburburan Annabin da Sahabban na sa biyu a dakin Rauda din.
4. Ginin dakin da fiyayyen halittar yake ciki an yi shi ne da bakin dutse wanda kuma babu kofa a tare da shi sai dai wata 'yar taga da aka yi wa kwalliyar zinare.
5. Wasu bata gari sun taba yin kokarin sace gangar jikin fiyayyen halittar a shekarun baya wanda hakan ne ma ya jaza aka yi wa kabarin na sa garkuwa da narkakken bakin karfe.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng