Yanzu-yanzu: Obasanjo, Olu Falae, Doyin Okupe suna ganawar sirri
A yanzu haka akwai wani ganawar sirri tsakanin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo; shugaban jam’iyyar Social Democratic Party, Cif Olu Fale, tsohon kakakin Jonatha, Dr Doyin Okupe suna wata ganawar sirri a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.
Cif Olu Falae wanda ya dade yana kai ziyara ga manyan masu ruwa da tsaki domin zaben 2019 ya isa gidan Obasanjo ne misalin karfe 12 na rana.
Sauran wadanda ke cikin ganawar sune tsohon dan takaran gwamnan jihar, Gboyega Nasiru Isiaka; tsohon kakakin Goodluck Jonathan, Cif Doyin Okupe; ddan takaran gwamnan jihar, Sina Kawonise, da sauran su.
Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar PDP sun sheka aya zuwa jam'iyyar SDP sanadiyar rikicin da yaki ci yaki cinyewa a cikin PDP.
KU KARANTA: Dalilin da yasa EFCC da DSS da kuma hukumar liken asiri ta kasa NIA suke fada a junansu
Daga cikin wadanda suka canza sheka sune Farfesa Jerry Gana, Farfesa Tunde Adeniran da sauransu. Wannan abu ya karawa jam'iyyar SDP karfi har ta fara ganin za ta iya taka rawan gani a siyasan Najeriya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng