Gwamnatin tarayya ta janye zargin da take yiwa ma’aikacinta akan motocin alfarma 86 da gidaje da yake dasu

Gwamnatin tarayya ta janye zargin da take yiwa ma’aikacinta akan motocin alfarma 86 da gidaje da yake dasu

- Gwamnatin tarayya ta janye zargin da take yiwa Daraktan kudi na ma’aikatar wutar lantarki da ayyuka da gidaje, Ibrahim Tumsah bisa ga laifin kin bayyana motocin na alfarma 86

- Tumsah ya gurfana a gaban kotun tarayya dake birnin tarayya tare da kaninsa Tijani, wanda yana daya daga cikin ‘yan kwamitin shugaban kasa na Arewa maso Gabas

- Wadanda ake zargin basu amsa laifin da ake zargin su da aikatawa ba, wanda kwamitin shugaban kasa na bincike da gano kayayyakin mutane wanda Okoi Obono-Obla yake jagoranta

Gwamnatin tarayya ta janye zargin da take yiwa Daraktan kudi na ma’aikatar wutar lantarki da ayyuka da gidaje, Ibrahim Tumsah bisa ga laifin kin bayyana motocin na alfarma 86 da gidaje da yake dasu.

Tumsah ya gurfana a gaban kotun tarayya dake birnin tarayya tare da kaninsa Tijani, wanda yana daya daga cikin ‘yan kwamitin shugaban kasa na Arewa maso Gabas kuma tsohon Sakataren tarayya na jam’iyyar APC.

Gwamnatin tarayya ta janye zargin da take yiwa ma’aikacinta akan motocin alfarma 86 da gidaje da yake dasu
Gwamnatin tarayya ta janye zargin da take yiwa ma’aikacinta akan motocin alfarma 86 da gidaje da yake dasu

Wadanda ake zargin basu amsa laifin da ake zargin su da aikatawa ba, wanda kwamitin shugaban kasa na bincike da gano kayayyakin mutane wanda Okoi Obono-Obla yake jagoranta.

Kafin a fara sauraron karar a kotun, Lauyan gwamnatin tarayyar, Mr Festus Keyamo, ya rubuta cewa gwamnatin ta janye karar.

A wancan zaman da akayi wadanda ake karar sun bukaci kotun da ta basu dama su daidaita a wajen kotu ba tare da anyi shari’a ba.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sanya muka kama ‘Yan Shi’a 115 cikin masu zanga-zanga - ‘Yan Sanda

Alkalin Nnamdi Dimgba ya soke zargin da ake yiwa wadanda ake zargin, ya kuma bayar dasu beli a kan kudi N20m da mutane biyu da zasu kawosu duk sanda kotu ta nemesu. Lauya cikin masu hukuncin ya bayyanawa Vanguard cewa gwamnatin tarayya zata sake yin kararsu idan ta gama bincikensu.

Gwamnatin tarayyar ta bayyana cewa a cikin motocin 86 da ta karba daga hannun wadanda ake zargin, 23 a ciki masu sulke ne kuma sababbi ne.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng