Tuna baya: Dalilan da suka sanya na rushe zabe 12 ga watan Yuli – Babangida

Tuna baya: Dalilan da suka sanya na rushe zabe 12 ga watan Yuli – Babangida

- Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Babangida ne ya shirya sannan ya rushe zaben shekarar 1993

- Zaben da ake kyautata zaton Marigayi MKO Abiola ne ya lashe shi

- Yanzu haka dai tsohon shugan kasar yayi bayani kan yadda aka haihu a ragaya

Tsohon shugaban Najeriya na mulkin Soja, Janar Ibrahim Babangida ya bayyana cewa, kamata yayi 'yan Najeriya su yaba mai sakamakon gudanar da zaben 12 ga watan Yuli, ba a rika sukar shi akan warware zaben da ake hasashen shi ne zabe mafi sahihancin da aka taba gudanarwa ba a kasar nan.

Tuna baya: Kamata yayi Yan Najeriya su yaba min domin gudanar da zaben 12 Yuni - Babangida

MKO Abiola

Babangida ya bayyana hakan ne, a cikin wata hira da yayi da Channels Television, inda yace, "A lokacin yakin hadin kan kasa, akalla mutane miliyan biyu zuwa uku ne suka rasa rayukansu domin tabbatar da zama kasa daya dunkulalliya". Anya munyi wa danda suka sadukar da rayukansu domin kasancewarmu guda adalci kuwa?

"Saboda haka ina ganin domin yin adalci ga wadanda suka bayar da rayuwarsu fansa ga Najeriya, ba mu da wani zabin da ya wuce mu yarda da abin da suka aikata, saboda sun miƙa rayukansu hadaya don tsare hadin kan kasar nan, domin ba batu ne da za’a nemi shawarar wani a hadin kai ba".

KU KARANTA: Cututtuka 9 da Ganyen Gwanda ke kawarwa a jikin dan Adam

Littafin tarihin rayuwa ta, "Mutane na iya kin karanta shi saboda zasu ce ai shugaban nan ne na Mulkin Soja, da yawa wasu kawai abinda zasu iya fada shi ne, soke zaben 12 Yuni 1993, kaga wannan zai sanya littafin ba zai daukaka ba. Amma idan har muna raye, insha Allahu zan fadi duk abubuwan da suka faru akan zaben 12 ga watan yuli 1993".

Babu wanda na taba gani yayi kokarin rubutu don wayar da kan Mutane akan maganar ta wata fuska ta daban, sai dai kawai soke zaben 12 ga watan yuli" Tsohon shugaban kasar ya bayyana cikin rashin jin dadi.

Tuna baya: Kamata yayi Yan Najeriya su yaba min domin gudanar da zaben 12 Yuni - Babangida

Tsohon Shugaban NajeriyaJanar Ibrahim Badamasi Babangida

Sai dai kawai maganar mun warware zabe, ba wanda yake gode mana balle a jinjina mana.

ya ce. "Na san yadda Abiola yake ji akan kasar nan kuma shi ma yasan yadda nake ji game da Najeriya domin muna tattaunawa kan Najeriya”.

"Ban son fada muku cewa duk da rushe zaben, mun fahimci juna da shi sosai, da a ce yadda muka fahimci kanmu da haka yan Najeriya suka gano to da ba haka ba, amma sai dai kash wasu ba sa son jin ma labarin balle har su fahimta".

Da yake bayyana ra'ayinsa yayin hirar tasa da aka haska ranar Litinin, kan wanda yake son ya zama shugaban kasa a 2019, cewa yayi, "Abin da nake so in gani shi ne wani Matashi mai baiwar abin da zan kira 'hudu a daya'.

Zabe mai zawa ina da burin ganin "Matashi wanda yana da hangen nesa kamar Obafemi Awolowo; Ina so in ga Matashi mai baiwa da fikira irinta Sardaunan Sokoto, Ahmadu Bello. Ina son ganin wanda yake da balaga da kuma ilimi kamar Dr Nnamdi Azikiwe. kuma ina so in ga wanda yake da kwarewa da wayo da irin Janar Olusegun Obasanjo, "Tsohon shugaban ya jaddada.

A cikin satin da ya gabata ne, Janar Babangidan ya karbibakuncin sabuwar jam'iyyar nan ta SDP wacce wasu ke hasashen ita da dan takarata zai marawa baya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel