Da zafi-zafi: Hukumar zabe mai zaman kanta ta rantsar da sababbin jami’ai 7
- Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta rantsar da sababbin kwamishinoninta guda 7
- Kwamishinonin wadanda aka rantsar zasu fara aiki a yau, zasuyi aikin har na tsawon shekaru biyar
- Farfesa Mahmood Yakubu, yace yana da tabbashin cewa zasuyi amfani da horon da suke dashi akan aikin su bayar da gudunmuwa sosai wurin ganin cewa zaben 2019 ya zama mafi inganci
Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta rantsar da sababbin kwamishinoninta guda 7. Kwamishinonin wadanda aka rantsar zasu fara aiki a yau, zasuyi aikin har na tsawon shekaru biyar.
Wadanda aka nada sune Dr Emmanuel Alex Hart, Mohammed Magaji Ibrahim, Dr Cyril Omorogbe, Dr Uthman Abdurrahman Ajidagba, Mr Segun Agbaje, Baba Abba Yusuf, da kuma Yahaya Bello.
Farfesa Mahmood Yakubu, yace yana da tabbacin cewa zasuyi amfani da horon da suke dashi akan aikin su bayar da gudunmuwa sosai wurin ganin cewa zaben 2019 ya zama mafi inganci a tarihin zaben Najeriya.
KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sanya muka kama ‘Yan Shi’a 115 cikin masu zanga-zanga - ‘Yan Sanda
A satin da ya gabata ne shugaba Buhari ya amince da nada sababbin kwamishinonin na hukumar zaben, a bayanin da yayi ta bakin sakataren gwamnatin tarayya Boss Gida Mustapha, ta hanyar Daraktan labarai na Ofishinsa Lawrence Ojabo.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng