Ciki da Goyo: Shan Paracetamol da Ibuprofen da Mata masu ciki keyi, na iya hana zuri'arsu haihuwa nan gaba
- Mata masu ciki na shan maganin gajiyar jiki ba tare da sanin matsalar da hakan ke jawowa jiki ba
- Wani sabon bincike ya gano irin illar da shan magungunan kashe gajiya ke yiwa jikin da Adam
- Magungunan na iya gadar da karancin haihuwa ga yayan da aka haifa yayin rainon cikin da aka sha kwayoyin kashe gajiyar
A wani bincike da aka gudanar, an gano cewa shan magungunan kashe gajiya da Mata masu ciki ke na mutukar zama illa ga rayuwar abinda ke cikin nasu da ma sauran zuri’ar da zasu fito ta tsatsonsu.
Binciken da jami’ar Edinburgh ta gudanar, yayi duba ne kan yadda kwayoyin da mata masu cike ke sha yayin da suka ji gajiya, irinsu Paracetamol da Ibuprofen.
Sakamakon binciken ya bayyana irin illar da kwayoyin keyi, ta hanyar kashe kwayoyin halittar dake cikin mahaifa da 40% idai har mai cikin ta sha magungunan na kimanin tsawon sati guda, amma binciken ya yace illar da Ibuprofen yake tafi yawa, domin kuwa yakan kashe kwayayan haihuwar da kusan rabi (50%).
Mata dai ana haifar su ne da duk kwayayan haihuwarsu a cikin mahaifa, kaga kenan idan saboda wannan shan kwayoyi aka haifesu da yan kadan to an tauye musu adadin yayan da zasu haifa anan gaba, a wani lokacin ma sukan iya zama bakarara (Juya). Inji masanan.
KU KARANTA: Hodijan! Qabila dake sa yayyen amarya dandana Ango kafin su bashi diyarsu
Kuma binciken yace illar bata tsaya ga yaya Mata zalla kawai ba, har da suma yaya Maza kwayoyin nayi musu illa, domin zai rage musu yawan adadin maniyyinsu.
Masu binciken sun gano cewa, shan irin wadannan magunguna na kawo sauye-sauye a kwayoyin halittar dan Adam, har ma ya bar masu tabon da za’a iya gadarsa.
A saboda haka yawan shan kwayoyin na iya haifar da karanci ko rashin haihuwar ga zuri’a kuma ana iya gadarsa.
“Muna kira gare su, da su bi a hankali wajen shan irin wadannan kwayoyi yayinda suke da juna biyu, su tabbata sun bi ka’idojin da Likita ya sharuddanta musu domin shan yan kadan a kuma kankanin lokaci”. A cewar Dr Rod Mitchell, wanda shi ne ya jagoranci binciken.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku
ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng