Karatun addini bai ci baya ba kamar yadda wasu ke nunawa - Sultan

Karatun addini bai ci baya ba kamar yadda wasu ke nunawa - Sultan

- Sultan na Sokoto, Alhaj Sa’ad Abubakar III, yace karatun addini bai ci bay aba kamar yadda wasu ke nunawa

- Abubakar ya bayyana cewa bazamu bari mutane su ringa cewa bamu san abunda mukeyi ba, saboda muna da ilimi, a wurin bikin Sheikh Adam Al-Ilory, a jami’ar Legas

- Al-Ilory shine wanda ya kirkiro Markaz Agege Centre for Arabic and Islamic, a jihar Legas

Sultan na Sokoto, Alhaj Sa’ad Abubakar III, yace karatun addini bai ci ba yaba kamar yadda wasu ke nunawa, cewa ilimin addini yaci baya sosai a cikin al’umma.

Abubakar ya bayyana cewa "bazamu bari mutane su ringa cewa bamu san abunda mukeyi ba, saboda muna da ilimi," ya fada hakan ne a wurin walimar tinawa Sheikh Adam Al-Ilory, a jami’ar Legas.

Al-Ilory shine wanda ya kirkiro Markaz Agege Centre for Arabic and Islamic, a jihar Legas, wanda yana cikin shahararrun malama Najeriya har bayan rasuwarsa shekarar 1992.

Sultan ya bayyana cewa Al-Ilory babban malami ne kuma shahararren maruci wanda ya koyar da iliminsa ga mabiyansa harma da masu tasowa.

Karatun addini bai ci baya ba kamar yadda wasu ke nunawa - Sultan
Karatun addini bai ci baya ba kamar yadda wasu ke nunawa - Sultan

Gwamnan Jihar Ogun, Ibikunle Amosun, yace babu hanyar datafi dacewa a bayar da tarihin musulunci wadda tafi ta hanyar ilimi. Ya kara da cewa Makarantar Markaz za’a ginata a garin Abeokuta tare da goyon bayan Sultan.

KU KARANTA KUMA: Nyass ba Allah ba ne, masu danganta shi da Allah sun kafirta - Inji Sheikh Sani Yahaya Jingir

Shugaban Majalissa, Bukola Saraki yace zamuyi iya kokarinmu muga cewa an kaddamar da wannan makaranta don cigaban addini, yayinda shi kuma mataimakin shugaban jami’ar Dr. Wale Babalakin yace, ana bukatar kudi idan anaso a ida gina jami’ar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel