Dan achaba ya kashe kansa bayan an ci babur dinsa a cacan kwallon Barcelona da Roma
Wani matashi dan achaba a garin Ilori, babban birnin jihar Kwara, mai suna Ekene Ugwuanyi, ya hallaka kansa sanadiyar cin babur dinsa a cacan was an kwallon kafa tsakanin kungiyar kwallon Barcelona da AS Roma.
Wannan abu ya faru ne a wani gidan kallon kwallo da ke unguwan Oko-Erin yayinda aka buga was an gasar Champions League tsakanin FC Barcelona da AS Roma.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa dan shekara 25 din ya shiga caca ne da babur na cewa idan kungiyar kwallon Barcelona bata samu nasara kan Roma ba, ya bayar da babur din.
Abin mamaki, kawai sai kungiyar Roma ta lallasa Barcelona a ranan.
Kaninsa, Okechukwu, yace kawai ya ga kofar dakin yayansa a bude kuma ya ganshi ya rataye kansa.
Rahoto ya nuna cewa wannan matashi ya yi hakan ne saboda babur dinsa daya kenan kuma da ita ya ke sana’a domin cin abinci.
KU KARANTA: Yadda kannen Amarya ke dana ango don gwada kwarinsa a wata kabila
Wata majiya ta kara da cewa ai babur din ba tasa bace. An bashi ajiya ne kawai sai yaje yayi caca da ita.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng