An kama tsohuwa ‘yar shekara 75 zata shiga da kwayoyi kasar Saudiya
- Wata tsohuwa ‘yar kasar Misra ta shiga hannun hukuma a filin jirgi na Yanbu dake kasar Saudiya bayan tazo da sunan zatayi Umrah
- Tsohuwar mai suna Saadeya Hammad ‘yar kauyen Darin, a garin Nabaruh dake Misra, kamun nata ya janyo zanga-zanga a kauyen nasu
- Mutanen kauyen nasu sun bayyana cewa makwabcinta ne ya yaudare ta inda yace wani dan kasuwa ne na kasar Saudi ya dauki nauyin biya mata komai na zuwa Umrah don tayi ziyara
Wata tsohuwa ‘yar kasar Misra ta shiga hannun hukuma a filin jirgi na Yanbu dake kasar Saudiya bayan tazo da sunan zatayi Umrah.
Tsohuwar mai suna Saadeya Hammad ‘yar kauyen Darin, a garin Nabaruh dake Misra, kamun nata ya janyo zanga-zanga a kauyen nasu, inda mutanen suka taru a kofar gidanta don nuna rashin amincewarsu akan zargin da akewa tsohuwar.
Mutanen kauyen nasu sun bayyana cewa makwabcinta ne ya yaudare ta, inda yace wani dan kasuwa ne na kasar Saudi ya dauki nauyin biya mata komai na zuwa Umrah, a cikin mutane 15 da ya zaba zai biyawa, domin su kai ziyara a kasar ta Saudiya.
Hukumar ‘Yan Sanda tayi nasarar kama mutane uku wadanda ake zargi da hannu a aciki,Abdallah Mohammad Al Manzalway, da kanwarsa Jariah Abdallah Al-Manzalway, da kuma mijinta Muhammad Fayek Jafar.
KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa nake takarar gwamna a Kano – Zaura
Bayan haka kanwar tasa ta bayyan cewa yayan nata Abdallah Al-Manzalway ya baiwa Saadiya Hammad jaka dauke da kwayoyin na tramadol 17,000, kuma ya fada mata cewa idan ta isa kasar Saudiyya ta bawa dan kasuwar wanda ya biya mata kudin zuwan Umrah.
Sannan wanda keda kamfanin zirga-zigar mutane zuwa kasahe na kasar Misra, Mahmoud al Tunsi ya bayyana bidiyo mai daukar cikin Ofishinsa wanda ya nuna lokacin da Al-Manzalway yake kokarin karbarwa Hammad takardun tafiya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng