Yanzu-yanzu: Rikici ya barke tsakanin yan sanda da yan Shi'a a Abuja, mutum daya ya mutu

Yanzu-yanzu: Rikici ya barke tsakanin yan sanda da yan Shi'a a Abuja, mutum daya ya mutu

Wani mumunan rikici ya barke tsakanin jami'an yan sandan Najeriya da yan kungiyar Shi'a a babban birnin tarayya Abuja da ranan nan.

Idanuwan shaida sun bayyana cewa jami'an yan sandan sun watsa wa yan shi'an barkonon tsohuwa ne yayinda suke zanga-zanga a farfajiyar Unity Fountain, kusa da Transcorp Hilton Abuja.

Yan Shi'an sunce ba za su daina wannan zanga-zanga ba muddin gwamnatin shugaba Buhari bata saki shugabansu, Ibrahim El Zakzaky ba.

Yanzu-yanzu: Rikici ya barke tsakanin yan sanda da yan Shi'a a Abuja, mutum daya ya mutu

Yanzu-yanzu: Rikici ya barke tsakanin yan sanda da yan Shi'a a Abuja, mutum daya ya mutu

An kashe akalla mutum daya yanzu. Wani idon shaida ya bayyanawa manema labarai cewa yan sanda ne suka harbeshi yayinda yake kokarin shiga cikin farfajiyar Unity Fountain.

KU KARANTA: Wanda ya tsaya takara a matsayin mataimakin Buhari a 2011 yayi tir da Gwamnatin sa

Har yanzu ana nan ana artabu yayinda yan sanda basu gushe suna watsa musu ruwan zafi ba kuma yan Shi'a sun ki barin wajen.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel