Tsallake Rijiya da baya: An kusa kashe wani Saurayi bayan ya yiwa budurwarsa wanka da guba

Tsallake Rijiya da baya: An kusa kashe wani Saurayi bayan ya yiwa budurwarsa wanka da guba

- Wani Matshi ya zubawa budurwar guba a fuskarta, bayan ya zarge ta alaka da wani

- Sai dai wasu gungun fusatattun matasa sun kai masa farki, da kyar yan sanda suka cece shi

Wani saurayi dan shekara 33 da aka bayyana sunansa da Lukman Madoti, ya tsallake rijiya da baya, sakamakon saura kiris wasu matasa su aike da shi lahiri.

An dai rawaito cewa matashin ya yiwa budurwar tasa wanka da gubar ne a satin da ya gabata, a unguwar Toyin Muyibi dake yankin Akala na jihar Lagos.

Tsallake Rijiya da baya: An kusa kashe wani Saurayi bayan ya yiwa budurwarsa wanka da guba

Tsallake Rijiya da baya: An kusa kashe wani Saurayi bayan ya yiwa budurwarsa wanka da guba

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa, wanda ake zargin ya zubawa budurwarsa guba a fuska ne bayan da ya zarge ta da kwanciya da wani Namijin.

An dai rawaito cewa, budurwar tayi duk wani yunkuri a dakinta nayi masa bayani kan cewa zargin nasa ba dai-dai ba ne, amma yaki yarda ya gamsuwa da hujjojinta.

Amma sai dai saurayin nata ya fice daga dakin yana mai cewa “Sai ya koya mata darasi”.

Wani wanda abin ya faru a gaban idonsa, ya shaidawa majiyarmu cewa, bayan wannan hatsaniyar da ta faru tsakanin masoyan biyu ne, aka ga Lukman a layin Alhaji Lasisi, yazo domin cika waccan alkawarin da ya dauka na yin maganinta, inda daga zuwansa baiyi wata-wat ba ya ya kwara mata ruwan gubara fuskarta.

KU KARANTA: Halima daya daga cikin direbobin manyan motan Dangote

Koda mutanen wurin suka ga haka, sai su kayi ca kansa suka fara masa lugude. Da yake da kwanansa a gaba, sai yan sanda sukai nasarar cetonsa daga hannun fusatattun matasan, amma sai dai ya samu muggan raunuka na duka da kuma saran adda. Kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Yayin da ita kuma budurwar aka garzaya da ita babban asibiti Gbagada domin yi mata magani, kasancewar ta samu rauni sosai a dalilin zuba mata gubar.

Shi kuma saurayin nata aka kai shi wani asirtattacen asibiti don yi masa magani, kuma yan sanda na cigaba da gadinsa domin kar wadancan hasalallun matasan su sake dawowa.

Kakakin rundunar yan sanda na jihar ta Lagos Chike Oti, ya tabbatar da faruwar lamarin, kana kuma yace, yanzu haka suna cigaba da bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku

ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

https://business.facebook.com/naijcomdaily/posts/2059119010967505

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku

ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel