Mahaifina ya kona mani kaya saboda na yarda da Yesu Almasihu - Sanata Binta

Mahaifina ya kona mani kaya saboda na yarda da Yesu Almasihu - Sanata Binta

- Sanata mai wakiltar mazabar Adamawa ta Arewa, Mrs Binta Masi Garbaa ranar Lahadi ta bayyana yadda mahaifinta ya kona mata kaya saboda ta bayar da rayuwarta ga Yesu Almasihu

- Ta bayyana hakane lokacin da suke bikin nuna godiya ga Ubangiji bisa ga zagayowar ranar haihuwarta a cocin Chapel of Praise International

- Binta ta fashe da kuka bayan tinawa da tayi da yanda ta fuskanci tsangwama da rashin kauna daga maifinta bayan amincewa da tayi da Yesu Almasihu a matsayin Ubangijinta kuma macecinta a ranar Lahira

Sanata mai wakiltar mazabar Adamawa ta Arewa, Mrs Binta Masi Garba a ranar Lahadi ta bayyana yadda mahaifinta ya kona mata kaya saboda ta bayar da rayuwarta ga Yesu Almasihu.

Ta bayyana hakane lokacin da suke bikin nuna godiya ga Ubangiji bisa ga zagayowar ranar haihuwarta a cocin Chapel of Praise International, inda ta cika shekara 50 a duniya.

Binta ta fashe da kuka bayan tinawa da tayi da yanda ta fuskanci tsangwama da rashin kauna daga maifinta bayan amincewa da tayi da Yesu Almasihu a matsayin Ubangijinta kuma macecinta a ranar Lahira.

Mahaifina ya kona mani kaya saboda na yarda da Yesu Almasihu - Sanata Binta
Mahaifina ya kona mani kaya saboda na yarda da Yesu Almasihu - Sanata Binta

Mataimakin shuagaban kasa a jawabinsa yayi kira da yiwa shuwagabanni addu’a, musamman kiristoci dake rike da manyan Ofisoshi na gwamnati a fadin Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Barayi kadai ke zama shuwagabannin kasa a Najeriya- Balarabe Musa

Yace ayi addu’a ta musamman ga sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha da shugaban ma’aikata na tarayya Wninifred Oyo-Ita da sauran wadanda ke rike da manyan mukamai a gwamnatin Buhari, don suyi abunda ya kamata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng