Idan kaga mun sha ruwa, to ruwan sama akayi - Labarin wata yar Chibok da tayi shekaru 3 hannun Boko Haram
Lydia Joshua, daya daga cikin yan mata 276 da yan Boko Haram sukayi garkuwa da su a makarantan Chibok, jihar Borno a ranan 14 ga watan Afrilu 2014, ta bayyana cewa a shekaru ukun da tayi a hannun su, ruwan sama kawai suke sha.
Lydia Joshua na cikin yan matan da aka saki bayan cinikin da gwamnati tayi da Boko Haram a shekaran 2017.
Yanzu tana kokarin dawo da rayuwarta kamar yadda yake da bayan shekaru 3 cikin wani irin halin rayuwa na daban a hannun yan ta'adda.
'Yar uwar Lydia, Matina Butu, ta bayyanawa jaridar The Cable halin da yan matan suka shiga a hannun Boko Haram.
"Yan matan sun sha bakr wahala musamman wadanda suka ki auren yan Boko Haram. Yan ta'addan zasu bukaci duk mai son aurensu ta daga hannu, wadanda suka ki kuma za su sha bakar yunwa."
“Idan akayi ruwan sama, ruwa zai bugesu har tufafinsu ya bushe a jikinsu. Kana sai anyi ruwan sama suke samun ruwan sha."
"A kasa suke kwana. Allah ne kawai ya tsiratar da rayuwan Lydia. Ta bayyana min cewa ganye suke ci, tunda ko an basu abinci ba ya isa. Sai lokacin da aka fara tattaunawa da gwamnati kan sakesu aka fara basu abinci isasshe."
KU KARANTA: Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gana da shugaban kasar Amurka
Lydia ta bayyanawa yar uwarta cewa suna bacci wajen da akwai macizai, sai suyi kwanaki ba tare da abinci ba kuma su dinga yi wa yan Boko Haram dinki.
ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng