Zaben 2019: Abokanan Buhari ne basa fada masa gaskiya da suka ce ya nemi tazarce

Zaben 2019: Abokanan Buhari ne basa fada masa gaskiya da suka ce ya nemi tazarce

- Koda Buhari yayi amfani da karfin mulki wajen zarcewa yan Najeriya tabbats za suyi masa bore

- A baya ma Obasanjo yayi yunkurin zarcewa a karo na uku bai yi nasara ba

- A lokacin da wasu suke kira da a sauya fasalin Najeriya mai yasa bai saurare su ba sai yanzu zai ce wasu ne suka bukaci ya zarce

Wani babban Malamin addinin Kirista, Archbishop emeritus Anthony Olubunmi Okogiena na jihar Lagos, ya bayyana cewa abokanan shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ke bashi gurguwar shawarar sake tsayawa takara a 2019. Domin kuwa a cewarsa, yan Najeriya sun gaji da shi (Buhari) kuma zasu yi amfani da kuri’arsu wajen canza sa.

A matsayinsa na shugaban kasa, zai iya murde zabe ko yabi wata hanya ya sake komawa, amma nasan cewa, mutanen Najeriya yanzu hankalinsu ya karkata ne ga sauya shi. Muryar al’umma hakika muryar Ubangiji ce, kuma al’ummar sun ce basa so, wannan kullum sai na karanta a jarida, Mutane na cewa Buhari bai yi aikin da za’a kara zabarsa ba”. A saboda haka ya rage nasa ya sake karatun ta nutsu.

Zaben 2019: Abokanan Buhari ne basa fada masa gaskiya da suka ce ya nemi tazarce
Zaben 2019: Abokanan Buhari ne basa fada masa gaskiya da suka ce ya nemi tazarce

Babban Malamin ya cigaba da cewa, shugaba Buhari na da yancin tsayawa takara ko yayi duk abinda rasa yake so, haka-zalika su ma yan Najeriya na da yancin zabar wanda suke so kamar yadda yake faruwa a sauran kasashen duniya. “Kuma sun ce basa son ya zarce saboda bai yi rawar gani ba, amma idan yana son ta karfin tsiya sai ya zarce, to ga fili ga mai doki”.

KU KARANTA: Zaben 2019: Kawai ka manta da batun a sake zabenka

Duk da cewa ni ba dan siyasa bane, amma ai muna ji kuma muna gani irin yadda Jam’iyyar PDP ta ce sunayen barayin da APC suka fitar ba dai-dai ba ne, domin babu dan jam’iyyar adawa ko daya. Amma mai APC suka ce? Sun kasa ma mayar da martani. “Ko dai ina tunanin ko sunyi zaton yan Najeriya bacci suke”.

Zaben 2019: Abokanan Buhari ne basa fada masa gaskiya da suka ce ya nemi tazarce
Zaben 2019: Abokanan Buhari ne basa fada masa gaskiya da suka ce ya nemi tazarce

Ni da kaina saunawa ina rubutu a jaridu kan yadda abubuwa suke tafiya amma babu wanda ya taba amsawa. Ni badan siyasa bane, amma ina tabbatar muku yanzu ba da ba ne, yadda muke siyasa ya canza sosai, don yanzu yan Najeriya ba za su yarda da irin wannan cin kashin ba.

Mutane suna cikin matsanancin hali, kullum kashe su ake yi amma shugaba Buhari bai ce komai ba. Littattafai masu tsarki sun umarce mu da mu so makwabtanmu, shin wadanda ake kashewa ba makwabtanmu ba ne?

“To ko shugaban kasa yayi karfa-karfa ya koma yan Najeriya zasu masa bore, don baza su amince ba” ina jaddada wannan inji Archbishop Anthony

Wasu na ganin cewa babu wanda zai iya maye gurbin Buhari, wannan ba haka ba ne. Muna da mutane na kwarai da zasu iya aikin ake da bukata. Idan har dagaske ne, kiran al’umma ne yasa shi ya sake tsayawa takara, mai yasa sanda wadansu suke kira a sake fasalin kasar nan bai amsa kira ba? A baya ma ai Obasanjo yayi niyyar zarcewa karo na uku amma bai samu nasara ba mai yasa.

Kira na ga yan Najeriya shi ne, su fita suje suyi rijistar zabe kuma su tabbata sun kada kuri’arsu a lokacin zaben, domin zabar sabon shugaban kasar da zai magance musu matsalar da suke fama da ita.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku

ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng