Mata na son su rinka hada sahu da maza a wajen sallah
Rahotani sun kawo cewa mata a birnin Santabul suna gudanar da wata fafutuka.
Suna kalubalantar dokokin tsarin raba sahun mata da maza a wajen sallah.
Zeynep dalibar jami’a, Idan kayi sallah a wani waje da ba ka ganin liman da sauran masallata, zaka ji kamar baka cikin sauran masallatan.
Ana ware wajen sallar mata akan bene chan bayan masallaci.
Shafin BBC Hausa ta rahoto cewa a watan Maris an kora wa mata daga masallaci sakamakon kin amincewa da ware wajen mata daban.
KU KARANTA KUMA: Ku jira shugabancin 2023 domin bazaku iya da Buhari ba – Tsohon gwamna a mulkin soja ga Atiku da sauran masu neman takara
Hakan ne ya janyo fara fafutukar mata a masallatai.
A cewar wata daliba kuma suna aiki da karatu tare da maza amma sai a raba su wajen Sallah.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng