Tanka Yakasai, Ghali Na’Abba, Babangida Aliyu sun yi kus kus da IBB, karanta abinda suka tattauna
Shuwagabannin kungiyar dattawan Arewa a karkashin jagorancin fitaccen dan siyasan jihar Kano, Alhaji Tanko Yakasai sun yi kus kus da tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida a yayin wata ziyara da suka kai masa a gidansa dake saman Dutse a garin Minna na jihar Neja.
Daga cikin tawagar da ta kai wannan muhimmin ziyara akwai tsohon Kaakakin majalisar wakilai, Alhaji Umar Ghali Na’Abba, tsohon ministan Jonathan Bala Muhammed,Muhammed Abba Gana, Mustapha Bello da Sanata Waku.
KU KARANTA: Bamu gane ba, anyi yamma da kare: An kama wani mai adawa da Buhari a yayin zanga zangar yan Shia
Daily Trust ta ruwaito Tanko Yakasai ya bayyana manufar kafa kungiyar a matsayin don hada kan al’ummar Arewa, tare da kara dankon siyasa da na al’adu a tsakanin jama’an Arewa gaba daya, ya kara da cewa sun kafa kungiyar ne a watan Feburairu na shekarar 2016.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Dattijoj yana cewa: “Duk da cewa mun kafa kungiyarce bayan zaben 2019, bata da wani alaka da siyasa, hangen nesanmu ya wuce haka, don haka mu ba reshe bane na wata jam’iyyya. Amma muna da sha’awar tabbatar da ganin an samar da ingantattun yan takarkaru a dukkana matakai. ”
A nasa jawabin, tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida ya jinjina ma shuwagabannin kungiyar da suka yi namijin kokarin kafa ta tun da farko, sa’annan ya jaddada goyon bayansa ga kudirin wannan kungiya.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng