Aure: Ku taimake ni ku raba aure na da kwartuwar Mata ta, Inji wani Pasto

Aure: Ku taimake ni ku raba aure na da kwartuwar Mata ta, Inji wani Pasto

- Wani Pasto ya ruga Kotu domin a taimake shi a raba shi da Matarsa mai bin Maza

- Amma sai dai Matar ta shi ta ce ai shi ne mai neman Mata ba ita ba.

- Alkali ya ba su lokaci domin su sasanta kansu ko kuma ya raba auren nasu

wani malamin choci mai suna Pastor Joshua Ibeneme, mai shekaru 53 ya bukaci kotu da ta raba auren shi da matarsa, duk kuwa da cewa sun shafe kimanin shekaru 21 tare, a cewarsa Matar tasa mai suna Uzoamaka, na lalata da wasu mutane su biyu da suke zuwa bauta chocinsa.

“Mata ta kwartuwa ce, domin tana saduwa da mazan da suke zuwa choci na, sai fadawa wasu suke yi sunyi lalata da ita, wai tana tayar musu da hankali. Kuma idan nayi tafiya na dawo karamin dana yana fada min wasu suna zuwa suna daukarta ko sauke ta a mota. Kuma dama har wahayi aka yi min lallai-lallai na sake ta ko kuma zata yi sanadiyyar tarwatsewar harkokin majami’ata”. A cewar Ibeneme.

Aure: Ku taimake ni ku raba aure na da kwartuwar Mata ta in wani Pasto
Aure: Ku taimake ni ku raba aure na da kwartuwar Mata ta in wani Pasto
Asali: UGC

Paston ya cigaba da cewa, “Shekaru biyar kenan Matar tasa taki yarda ya tara da ita, kullum in ya kusance ta sai ta rika nemo dalilan da zai sanya ya rabu da ita, a karshe ma har tayi kaura daga turakarsa, amma kuma taje tana yawon ta zubar, tan akwanciya da wasu mazan daban, gata kuma da yawan kunyata ni a gaban mutane, da mugun zargi, duk matar da tazo waje na neman shawarwari ko addu’a sai ta ce wai lalata nake da su”.

Sai tana zarginsu da cewa, wai yan mata na ne, kuma soyayya suke da ni, har ta kai ma tana iya binsu har gida ta same su tana fada da su. Irin wannan munanan dabi’un nata sai da suka korar min mambobin choci na suka daina zuwa sosai, kuma wani abin Karin bakinciki ma shi ne yadda matar tasa Uzomaka ta sanya yayansu suka juya masa baya. ”Ba sa girmama ni kodan, kai hatta aike in nayi musu basa zuwa sai mamasu ta basu umarni”. Inji Paston

KU KARANTA: Dandalin Kannywood: 'Yan sanda sun cika hannuwan su da 'yan fim 28 suna 'shutin' a Zariya

A saboda haka ne Paston ya roki kotun da ta taimaka ta raba shi da wannan matar tasa, “A taimaka a raba auren nan don bana son ta yanzu ko kadan”.

Amma a nata jawabin Matar Paston Uzomaka cewa tayi, Babu wani wanda tayi lalata da shi sai dai ma shi Maigidan nata tabbas yana shawagin tsuntsayen neman mata.

Ta ce, “Matan da Mijin nawa yake so ne babbar matsalar da ta sanya muke fada kuma naga hankalinsa ya karkata gare su. Amma ni banyi lalata da Maza biyun da yake zargi na da suba ba, kawai dai suna son bata min suna ne, don Maigidan nawa saurayin daya daga matar su ne”.

Matar Paston Uzomaka mai shekaru 45,wadda Malama ce tace, Mijin nata ya samu matsala ne ta rashin iya gamsar da ita tun shekaru biyar da suka gabata. Kuma yana ce min “Karuwa a gaban Mutane, sannan yanzu yace na sanya Yaranmu sun juya mai baya”. Wanda duk bah aka ba ne.

Sannan ta roki kotun da ta amsa bukatar mijin nata ta son a raba su, domin kowa ya kama gabansa, amma dai a cewarta har yanzu tana son Mijin nata.

Daga karshe Alkalin kotun Mr Akin Akinniyi, dake zamanta a Igando dake Jihar Lagos ya shawarci ma’auratan da su taimakawa su daidaita junansu domin ceton rayuwar auren nasu mai shekaru har ashirin da daya, idan kuma hakan bai samu ba to su dawo ranar 10 ga watan mayu domin yanke hukunci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku

ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng