Da dumin sa: Dakarun sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara akan 'yan Boko Haram
Rundunar dakarun sojojin Najeriya a jiya ta bayar da labarin samun nasarar da suka yi na fatattakar wasu 'yan Boko Haram tare da kashe bakwai daga cikin mayakan su a wani gumurzu da akayi a cikin dazukan jihar Borno.
Kanal Onyema Nwachukwu dake zaman mataimakin daraktan dundunar tabbatar da zaman lafiya dake yaki da 'yan ta'addan ne dai ya sanar da hakan ga manema labarai a can garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
KU KARANTA: Majalisar wakilai za ta binciki ministan Buhari
Legit.ng ta samu cewa haka zalkika kamar dai yadda ya shaidawa majiyar mu, rundunar ta su ta kuma samu nasarar kama wani wanda ke yi wa 'yan ta'addan leken asiri mai suna Modu Chari.
A wani labarin kuma, Hukumar rundunar sojojin Najeriya a jiya ta fito ta karyata rade-raden da ke yawo musamman ma a kafafen sadarwar zamani na cewar wai tana nuna son kai a wajen daukar sabbin ma'aikatan hukumar da ke gudana a halin yanzu.
Babban daraktan rundunar da ke kula da harkokin hulda da jama'a da yada Labarai Birgediya Janar Texas Chukwu shine ya sanar da hakan a cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar a garin Abuja.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng