Buhari bai da nagartar ci gaba da shugabantar Najeriya a 2019 - Ghali Na'abba

Buhari bai da nagartar ci gaba da shugabantar Najeriya a 2019 - Ghali Na'abba

Tsohon kakakin majalisar wakillai ta Najeriya kuma dan asalin jihar Kano Alhaji Ghali Umar Na'abba ya bayyana cewa shi dai bai ga da wane ido shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari zai kalli 'yan Najeriya ba har ya ce su sake zabar sa a 2019.

Tsohon kakakin majalisar dai ya ayyana hakan ne a yayin wata fira da yayi da kamfanin jaridar Sun inda ya bayyana takaicin sa ga wadanda yace sun karfafawa shugaban kasar gwiwa don ya sake tsayawa takarar.

Buhari bai da nagartar ci gaba da shugabantar Najeriya a 2019 - Ghali Na'abba
Buhari bai da nagartar ci gaba da shugabantar Najeriya a 2019 - Ghali Na'abba

KU KARANTA: Buhari ba zai samu tikitin takarar 2019 kai tsaye ba - APC

Legit.ng ta samu cewa haka zalika ya kuma shawarci shugaban da ya sake yi wa kan sa karatun ta nutsu ya kuma janye wannan kudurin na sa tun kafin lokaci ya kure masa.

A wani labarin kuma, Gwamnatin jihar Bayelsa dake a shiyyar kudu maso kudancin Najeriya ta yi barazanar maka gwamnatin tarayya karkashin shugabancin Muhammadu Buhari a kotu idan dai har ta dage kan cewa sai ta fitar da kudin siyen makamai har Naira biliyan 360 kafin cire masu kudin su na kaso 13 cikin dari.

Wannan dai ya fito ne daga ofishin kwamishinan yada labarai na jihar Mista Daniel Iworiso-Markson a wata sanarwar manema labarai da ya fitar inda ya ke kara jaddada cewar dole ne sai an biya jihar su kason ta kafin a cire kudin makaman.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng