Karshen cin naman mata yazo: karanta alakar cin jan nama da kamuwa da ciwon daji

Karshen cin naman mata yazo: karanta alakar cin jan nama da kamuwa da ciwon daji

- Wani bincike da aka gudanar ya bayyana yadda rashin cin jan nama yake taimakawa wajen ragewa mata hadarin kamawa da cutar daji

Sakamakon binciken da aka yiwa akan wasu mata mazauna kasar England, ya nuna cewa, rashin cin jan nama na rage hadarin kamuwa da ciwon daji.

Binciken da aka yi domin gano alakar dake akwai tsakanin cin jan nama kamar na dabbobi da kaji ko kifi da mata keyi, na da alaka da kamuwa da ciwon kansa (colon da rectal cancer).

Karshen cin naman mata yazo: karanta alakar cin jan nama da kamuwa da ciwon daji
Karshen cin naman mata yazo: karanta alakar cin jan nama da kamuwa da ciwon daji

Sakamakon binciken ya nuna cewa, an gano duk matan da ke yawaita cin jan naman, kwayoyin dake haifar da kansar yafi saurin tasiri a jikinsu fiye da wadanda basa amfani da shi.

Wani marubuci da ya jagoranci binciken mai suna Dr Diego Rada Fernandez de Jauregui, wanda kuma guda daga cikin mambobin kungiyar dake kula da sinadaren abinci ta Nutritional Epidemiology Group (NEG) ta Jami’ar Leeds, yace sun mayar da hankali ne wajen gano yadda cin jan naman ya zama barazanar da ka iya jawo kansar.

KU KARANTA: Kowa ma ya sani wallahi miliyan 50 Atiku ya bani – Fati Mohammed ga magoya bayan Buhari

“Binciken namu na daga cikin bincike da aka gudanar a wannan fanni na alakar cin jan naman a kamuwa da kansar, amma sai dai har yanzu akwai bukatar a kara fadada binciken, domin samun muhimman bayanan iyalan dake dauke da kansar, da kuma tarihin kamuwar tasu domin ganowa da kuma lalubo hanyar magance ta”.

Karshen cin naman mata yazo: karanta alakar cin jan nama da kamuwa da ciwon daji
Karshen cin naman mata yazo: karanta alakar cin jan nama da kamuwa da ciwon daji

Binciken da aka gudanar ya nuna cewa, irin wannan kansa dai ita ce ta uku a jerin kansar da mata suka fi kamuwa da ita a kasar Birtaniya. Anyi hasashen cewa nan da shekarar 2030 mutane miliyan biyu da dubu dari biyu ne zasu iya kamuwa da wannan kalar kansar (colorectal cancer).

Nazarin dai yayi amfani da rukunin binciken da aka yi akan matan da yawansu yakai 32,147 na kasar England da Wales da kuma Scotland.

Shugabar kungiyar masu kula sinadaran cikin abinci (NEG) Farfesa Janet Cade, tace, “Binciken namu zai taimaka wajen karin haske kan yadda cin nama zai iya haifar da yiyuwar kamuwa da kansar. Kuma samun damar duba kundin rukunin binciken da mu kayi na matan UK, ya taimaka domin, za’a iya lalubo hanyar kariya ko magance kamuwa da kansar". Kamar yadda sciencedaily ta wallafa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng