An tsinci jaririn wata 8 a cikin randan ruwa
An tsinci gawan jaririn dan wata 8 mai suna Abdulaziz, a ranan Alhamis cikin randan ruwa a jihar Edo.
An tsinci gawan wannan jariri ne a gida mai lamba 53 Obakhavbaye Street, Benin City.
An samu labarin cewa mahaifiyar ta zaga bayan gida ne misalin karfe 6 na safe amma bata ga jaririn inda ta ajiyeshi.
Bayan anyi awa 3 ana nemanshi a cikin gidan. Daga baya aka ganshi cikin randa a mace.
Maigidan Ali Abubakar yayinda yake Sallan asuba ya ji mutane da iwu suna kuka.
Ali yace: “Abu ne mai wuya jariri ya bude randa ya shiga da kansa. Bamu san abinda ya faru ne abin mamaki” .
Wata makwabciya mai suna Blessing Akpo, ta bayyanawa manema labarai cewa Allah kadai zai iya tona asirin wadanda suka kashe wannan jariri.
“Ban taba ganin inda yayinda dan wata takwas ya bude randan ruwa ya tsunduma ciki ba sannan ya kulle,” Tace.
KU KARANTA: Dakurun soji sun kama wasu da ke da hannu cikin kashe-kashen jihar Taraba
Mahaifiyar ta kasa Magana saboda yadda abin yayi mata zafi.
Hukumar yan sandan sun garzaya wajen kuma suniya alkawari gudanar da bincike cikin wannan al’amari.
Asali: Legit.ng