Barayi 4 sun shiga hannu gami da motoci 11 da suka sata a jihar Filato

Barayi 4 sun shiga hannu gami da motoci 11 da suka sata a jihar Filato

A ranar Juma'ar da ta gabata shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa, hukumar 'yan sanda ta jihar Filato karkashin jagorancin kwamishinan ta Undie Adie, ta yi nasarar cafke wasu barayi 4 da suka addabi al'umma da laifin satar motoci har 11.

Barayi 4 sun shiga hannu gami da motoci 11 da suka sata a jihar Filato

Barayi 4 sun shiga hannu gami da motoci 11 da suka sata a jihar Filato

Wasu daga cikin motocin da barayin suka sace

Wasu daga cikin motocin da barayin suka sace

Kwamishinan 'yan sandan ya ce nan ba da jimawa ba za a gurfanar da su a gaban Kotu domin ta yanke ma su hukunci daidai da Shari'a.

KARANTA KUMA: Najeriya ta fara hangen yadda za ta amfana da $770m na tallafin UN

Babban jami'i Adie ya kara da cewa, an samu motocin 11 daga mutanen daban-daban a wasu sassa na jihohin Enugu da Ebonyi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel