Yau daren Isra'i da Mi'iraji a wurin musulmi, watau lokacin da annabi yaje sama ta bakwai

Yau daren Isra'i da Mi'iraji a wurin musulmi, watau lokacin da annabi yaje sama ta bakwai

- Yau ne Musulmin duniya ke bikin tunawa da maulidin Isra'i da Mi'iraji

- Ana so a raya daren da hailala da salatai da ibada da taqawa

- Musulmai sunyi imani cewa yau ne annabi ya hau dokin mai fiffike da ake kira buraqa domin zuwa sama ta bakwai

Yau daren Isra'i da Mi'iraji a wurin musulmi, watau lokacin da annabi yaje sama ta bakwai
Yau daren Isra'i da Mi'iraji a wurin musulmi, watau lokacin da annabi yaje sama ta bakwai

Yau ne Musulmin duniya ke bikin tunawa da maulidin Isra'i da Mi'iraji, Musulmai sunyi imani cewa yau ne annabi ya hau dokin mai fiffike da ake kira buraqa domin zuwa sama ta bakwai. Ana so a raya daren da hailala da salatai da ibada da taqawa.

A lokacin da ake wannan maulidi, musulmin duniya suna kara kaimin ibada da hailala da zikiri, domin neman falalar ubangijinsu Allah mai-sama.

A addinin na Islama dai, ansa rai annabi Muhammadu ya je Sama akan wani duko mai fiffike da mala'ila Jibrilu ya kawo masa, suka yi tafiya a sahara dare daya, zuwa kasar Israila, sannan suka kuma rankaya sama domin ganawa da Allah.

DUBA WANNAN: Duk wanda baya baiwa coci 10% daga dukiyarsa to wuta zai je- Babban Paston Najeriya

Wannan makala dai ga masu fikirar falsafa, suna da ja, inda suke ganin imani akwai doki mai tashi, ko kuma a tashi sama, baya nufin lallai hakan ya faru, don haka suke ganin musulmi sun yarda da gaibu ne kawai.

A zamunna a baya, an sha wannan bambarwa, inda wasu ke ganin to lallai sai dai ko a mafarki ne annabin yaje sama domin a zahiri, abiin da kamar wuya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng