Rikicin APC a jihar Kaduna: El-Rufai ya shirya kwashe inasa-inasa daga gidan gwamnati, zanyi takara insha Allahu – Shehu Sani

Rikicin APC a jihar Kaduna: El-Rufai ya shirya kwashe inasa-inasa daga gidan gwamnati, zanyi takara insha Allahu – Shehu Sani

Rikici tsakanin Gwamna Nasir El-Rufa’I da Sanata Shehu Sani ya fara ne tun wani sabani da suka samu a farin gwamnatin APC a 2015. Har yanzu an gaza sulhu tsakaninsu bal rikicin kara zurfafa ya keyi.

Rikicin ya samo asali ne tun lokacin da gwamnan jihar yayi wasu nade-nade ba tare da tuntuban Sanata Shehu Sani domin kawo nasa gudunmuwar ba. Daga nan aka fara soke-soke tsakanin juna har gabar ya munana.

Wannan abu ya kara zurfi ne yayinda aka fara jin kishin-kishin cewa Sanata Shehu Sani zai fito takara zaben gwamnan a 2019 domin doke Nasir El-Rufa’I amma dai ba’a ji daga bakin shi Shehu Sanin ba. Amma a yau ya bayyana alanta cewa lallai zai tsaya takaran kujeran gwamnan jihar a 2019 idan Allah ya yarda.

Ya yi wannan jawabi ne a wani martini da yayi kan sammacin da hukumar yan sandan jihar ta yi masa na zargin hannu cikin kisan kai. Shehu Sani yace:

“Maganan takaran Gwamna Zanyi Insha Allahu.Nasiru ka shirya kwashe kayanka daga gidan Gwamnati.Kama karyan ka da zaluncin ka ga talakawa Jahar Kaduna ya kusa zuwa karshe Insha Allah.”

Rikicin APC a jihar Kaduna: El-Rufai ya shirya kwashe inasa-inasa daga gidan gwamnati, zanyi takara insha Allahu – Shehu Sani

Rikicin APC a jihar Kaduna: El-Rufai ya shirya kwashe inasa-inasa daga gidan gwamnati, zanyi takara insha Allahu – Shehu Sani

Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisan dattawan Najeriya ya mayar da martini mai zafi bayan rahotanni sun yau cewa hukumar yan sandan Najeriya ta ambaci sunansa a cikin wadanda ake zargi da laifin kisan kai.

Hukumar yan sanda ta saki jawabin cewa ana zargin sanatan da hannu cikin wannan harin kisan kai a jihar Kaduna bisa ga wani jawabin kaset da aka ji.

KU KARANTA: Shehu Sani ya zargi El-Rufa’I da masa sharri, ya mayar da martini mai zafi

Kwamishanan yan sandan jihar Kaduna ya rubuta wasikan bukatan ganin sanatan ranan 30 ga watan Afrilu a shelkwatan hukumar na jihar Kaduna domin bayani da bincike.

Da jin wannan rahoto, sanatan ya mayar da martini mai zafi inda ya zargi gwamnan jihar Kaduna da kulla masa sharri.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel