Da dumin sa: Majalisar dattijai ta amince da sabbin nade-naden shugaba Buhari 3

Da dumin sa: Majalisar dattijai ta amince da sabbin nade-naden shugaba Buhari 3

Majalisar dattijan Najeriya a karkashin jagorancin Sanata Bukola Saraki ta amince tare da tabbatar da sabbin nade-naden da shugaba Muhammadu Buhari ya yi na wasu mambobin hukumar nan ta cigaban yankin Neja Delta watau Niger Delta Development Commission a turance.

Wadanda aka amince da su din dai sun hada da Mista Chuka Ama Nwauwa daga jihar Imo, Lucky Orimisan Aiyedatiwa daga jihar Ondo State sai kuma Nwogu N. Nwogu daga jihar Abia State.

Da dumin sa: Majalisar dattijai ta amince da sabbin nade-naden shugaba Buhari 3
Da dumin sa: Majalisar dattijai ta amince da sabbin nade-naden shugaba Buhari 3

KU KARANTA: Hukumar kwastam ta kai samame gidan Tambuwal

A wani labarin kuma, Babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) a Najeriya ta yi kira ga 'yan majalisar tarayyar kasar nan da su gaggauta kwace kambun shugaba Buhari tare da nada mataimakin sa a matsayin shugaban kasa biyo bayan tafiyar da yayi zuwa birnin Landan.

Wannan dai matakin dai a cewar jam'iyyar ya zama dole ne domin kare kasar nan daga shiga halin cakwakiyar shugabancin musamman ma dai ganin cewa shugaba Buhari din bai rubutwa majalisar ba kafin barin sa kasar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng