Tsaro: Ƴan sanda sun cafke uku daga cikin masu cewa ko a basu Miliyan uku duk wata ko su fasa butun mai
- Rundunar yan sanda tayi nasarar cafke tsagerun Niger Delta Avengers dake fasa butun mai suna kuma garkuwa da ma'aikatan hakar mai
- ACP Abba Kyari ne ya jagoranci farautar yan ta'addan
Rundunar ƴan sandan ciki masu nemo bayanan sirri dake aiki tare da babban sofeton ƴan sanda na kasa, sunyi nasarar damke wasu ƴan kungiyar tsagerun Niger Delta Avengers, waɗanda sunyi kaurin suna wajen barazanar garkuwa da ma'aikatan kanfanunuwan hakar mai.
Kamar yadda bayanai suka nuna, kame mutanen ya biyo bayan yawaiyar barazanar da kamfanin haƙar mai na Niger Delta Petroleum Resources, dake yankin Obumeze a ƙaramar hukumar Ahoada na jihar Rivers.
Bayan yawaitar wannan barazana ne, babban sifeton ƴan sandan Ibrahim Idris ya aike da dakaru ƙarƙashin nagorancin zakakurin ɗan sandan nan da ya kware wajen farautar masu garkuwa da Mutane ACP Abba kyari, zuwa fatakwal babban birnin jihar.
Dafarko dai ƴan ta'addan sunyi baraza na ne da cewa, a biya su Naira miliyan Ashirin kudi hannu sannan kuma ana biyansu Naira Miliyan Uku, duk wata a matsayin albashi.
KU KARANTA: Tashin hankali: Kotun duniya ta kasa-da-kasa na ta soma binciken Buhari kan laifuka 8
a cewarsu, kin bin wannan umarni nasu, zai haifar da fashe-fashen bututun mai da kuma sace ma'aikatan kamfanin haƙar man da ma lalata sauran kayan aikin kamfanin.
Ɗaya dag cikin waɗanda ake zargi mai suna LoveGod Chinuzioke, mai shekaru 27, ɗan asalin yankin ne na Obumeze a ƙaramar hukumar Ahoada dake jihar Rivers.
Yayinda Chinuzioke shi kuma ɗan maƙwabtan yankin da kamfanin haƙar man na NDPR, kuma ba ɗaɗewa aka bayar da belinsa daga gidan yarin nan mai cikakken tsaro na birnin Fatakwal ɗin, inda ake tuhumarsa da laifin fashi da makami da kuma garkuwa da mutane.
Bayan sanya komarsu da fara bincike game da irin yadda tsagerun ke karɓewa mutane kudi ne, suka samo lambar wayarsu. A cewar guda daga cikin manyan ma'aikatan kamfanin na NDPR.
Haka zalika, daya daga cikin waɗanda aka damkeakwai wani mai suna Justice Okolo, mai shekaru 25, kuma ɗan asalin ƙwaramar hukumar Aniocha dake jihar Delta.
Kuma Okolo shi ne wanda ya rubuta kuma ya aike da sakon barazanar ga kamfanin sannan ya amsa cewa, shi mamba ne na wata kungiyar riƙaƙƙun ƴan fashi da su kayi ƙaurin suna wajen aiwatar da mummunar sana'ar tasu a yankin na Ahoada da sauran maƙwabtan yankin, a yayin wannan kame dai har wayar da suka yi amfani da ita wajen aikewa da saƙon barazanar ita ma jaruman yan sandan sun samo ta.
Kuma har yanzu suna nan suna cigabada bincike don gano ragowar abokan ta'addancin nasu waɗanda suke dauke da harsasai da makamashi mai fashewa da sauran kayan da suke amfani da su wajen aikin nasu na ta'addanci kamar yadda jaridar The Eagle ta rawaito.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng