Bin Salman ya wasa wuka don yakar Shuraim daya da cikin limaman Kaaba

Bin Salman ya wasa wuka don yakar Shuraim daya da cikin limaman Kaaba

Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa Bin Salma ya sha alwashin toshe daya daga cikin manyan limaman masallacin Kaaba, sakamakon da’awah da yayi na cewa sauye-sauyen da yarima mai jiran gado yazo das u, sun sabama koyarwar shari’ar Musulunci.

Bin Salman ya sanar da cewa, ya rufe shafin twitter na Shuraim, inda ta nan ne limamin ke yi wa al’uma da’awa.

Yariman ya aikata hakan ne saboda gudun kada a rushe masa tsarin da ya fara daukowa na maida kasar Saudiyya babbar kasar zamani kamar yadda ya sanar da duniya.

Bin Salman ya wasa wuka don yakar Shuraim daya da cikin limaman Kaaba
Bin Salman ya wasa wuka don yakar Shuraim daya da cikin limaman Kaaba

Sheikh Saud Al Shuraim dai ya soki manufofin da Saudiyya ta dauka na gina wani katafaren filin shakatawa a gabar teku birnin Riyadh,inda mata za su dinka holewa a tsiraice, mulkin mallakar da Isra’ila ke ci gaba da yi wa Falasdinawa,da kuma sauran sauye-sauyen da Yariman ya zo da su.Abinda ya yi matukar bakanta wa Bin Salman.

KU KARANTA KUMA: Wanda akewa zargin fashi da makami yace yanawa wani dan Sanda aiki ne

Tun a lakoacin da ya karbi alakar mulkin Saudiyya, Bin Salman ya ci gaba da farautar manyan malaman kasar wadanda suka ki yin na’am da manufofinsa, ta hanyar taka hakkokin fadar bakunansu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng