Dubu ta cika: Yan sanda sun kama kamfanin lemon bogi, karanta kaji ko kana sha baka sani ba
- Yan sanda sun damke yan dafara masu hada lemon bogi
- Mutane biyar sun shiga hannu tare da kayan aikin hada lemon nasu
Kamfanin dillancin labarai ta kasa (NAN) ya rawaito cewa, Rundunar yan sanda ta jihar Lagos, tayi nasarar bankado wata masana’antar hada lemon jabu a Egbe-Afa a unguwar Igbogbo dake yankin Ikorodu, sanna kuma ta damke wasu mutum biyar da take zargi.
Kwamishinan yan sanda na jihar Lagos Edgal Imohimi, ne ya bayyana hakan ga manema labarai yayin da yake nunawa musu kayayyakin da masu laifin ke amfani da su wurin hada lemon jabun a jiya Laraba.
NAN ta rawaito cewa, daga cikin irin lemukan da yan damfarar suke hadawa sun hada; leman Malt da stout da kuma ethanol, kuma da zarar sun kammala hada wannan lemo sai dura shi a cikin babban mazubi a lodawa moto a kais hi inda ake durawa mota ta kai shi wurin da ake zubawa a kwalabe.
Kwamishinan yan sandan jihar Imohimi yace, zasu zurfafa bincike domin gano inda ake zuzzubawa a cikin kwalabe da kuma inda suke siyarwa.
KU KARANTA: Kwangilolin da Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya sa hannu a taron FEC na jiya
Rundunar yan sandan dai ta samu nasarar kama wannan haramtacciyar masa’anta ne da hadin gwuiwar mutanenmazauna yankin da suke taimakawa yan sandan samun bayanai. Kuma za’a rufe haramtacciyar masa’antar sannan a aika da sanfurin lemon bogin zuwa dakin bincike domin sanin illar da takan iya yi ga jiki da kuma gano abubuwan da suke amfani da shi wajen hadawa. A cewar kwamishinan.
“Nasarar kama kayan abu ne mai muhimmanci da yake nuna mana yadda mutanen unguwa zasu iya taimakonmu wajen tabbatar da tsaro kamar yadda ya kamata.”
Idan ba a manta ba dai a kwanan baya ne rundunar yan sandan sukai nasarar gano wani gida da ake hada jabun giya.
"Shi ma kuma a sakamakon irin hadina kai da muke samu ne daga wajen mutane mazauna yankin irin wannan al'mun dahan take faruwa. A saboda haka ina kara jan hankalin ku jama'ar Lagos da cewa, da zarar kunga wani abu da ake aikatawa ba dai-dai ba ko kuke zarginsa to kuyi maza ku sanar da hukuma." kwamishinan ya bayyana.
NAN ya rawaito cewa, an an kama sama da duro 100 da manyan mazuban da suke durawa. tare da gano kauyen da suke boye kayan aikin nasu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng