Yakubu Dogara ya nuna damuwarsa game da yawan mutuwa da akeyi a majalisar wakilai

Yakubu Dogara ya nuna damuwarsa game da yawan mutuwa da akeyi a majalisar wakilai

- Shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara ya bayyana damuwarsa akan yawan mutuwar da aka samu a wannan majalissa ta 8

- Dogara ya bayyana damuwar tisane a lokacin taron girmamawa da aka gudanar saboda mataimakin jagoran majalisar Buba Jibril

- Majalisar tayi amfani da wannan dama ta girmama Ali Wakili da Mustapha Bukar da Independence Ogunlewe wadanda duk suka rasu a majalissar

Shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara ya bayyana damuwarsa akan yawan mutuwar da aka samu a wannan majalissa ta 8.

Dogara ya bayyana damuwar tasane a lokacin taron girmamawa da aka gudanar saboda mataimakin jagoran majalisar Buba Jibril, wanda ya rasu akan aiki.

Majalisar tayi amfani da wannan dama ta girmama Sanata Ali Wakili daga jihar Bauchi, sai Sanata Mustapha Bukar daga jihar Katsina, sai kuma Hon. Independence Ogunlewe daga jihar Imo, wadanda duk suka rasu daga majalissa.

Yakubu Dogara ya nuna damuwarsa game da yawan mutuwa da akeyi a majalisar wakilai
Yakubu Dogara ya nuna damuwarsa game da yawan mutuwa da akeyi a majalisar wakilai

‘Yan majalissa da dama sunyi maganganu game da wadanda suka rasu akan halayensu na kirki da kuma abubuwan cigaba da suka gabatar a majalissa da kuma cigaban da suka kawo a siyasa.

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin Najeriya ta tasa keyar wasu manyan ‘yan ta’adda (hotuna)

Wadanda sukayi jawaban sun hada da shugaban majalisa Yakubu Dogara, da mataimakinsa Hon. Yussuff Lasan, sai Hon. Chukwuka Onyema, Hon. Nnenna Ukeje, Hon. Saheed Fijabi, Hon. Aminu shehu Shagari, da kuma Hon. Femi Gbajabiamila.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng