Martani mai zafi: Shekaru ukun Buhari tafi takwas din da Obasanjo yayi yana mulkin Najeriya

Martani mai zafi: Shekaru ukun Buhari tafi takwas din da Obasanjo yayi yana mulkin Najeriya

- Da alama Obasanjo ya debo ruwan dafa kansa sakamakon martani zafafa da yake sha daban-daban

- Sai da Obasanjoya shafe shekara guda yana yawan ta zubar a kasashen duniya a lokacin yana shugaban kasa inji Tony Momoh

Obasanjo na cigaba da shan zafafan martani tun bayan da yace shugaban kasa Muhammadu Buhari bai cancanci a sake zabarsa a karo na biyu ba, inda a baya-bayan nan tsohon shugaban narkakkiyar jam’iyyar CPC Prince Tony Momoh, yayi masa nashi martanin cikin zafafan kalamai a wata hira da yayi da Jaridar Independent.

A cewar Tony Momoh, Muhammadu Buhari ne sanadiyyar kasancewarsa a siyasa tun 2003, kuma ko yanzu Buhari ya daina siyasa to shi ma zai daina. Momoh dai na daga cikin wadanda su kayi nakudar haihuwar jam’iyyar PDP a watan Disambar 1998.

Martani mai zafi: Shekaru ukun Buhari tafi takwas din da Obasanjo yayi yana mulkin Najeriya
Martani mai zafi: Shekaru ukun Buhari tafi takwas din da Obasanjo yayi yana mulkin Najeriya

KU KARANTA: 'Yan bindiga cikin kakin 'yan sanda sun kashe DPO

“Ko kusa ai baza ka hada shekaru ukun Buhari da shekaru takwas din Obasanjo ba, shi Obasanjo ya shafe shakara guda yana yawon zagaya duniya, ya bar mulki a hannun mataimakinsa Atiku, bayan sun zarce kuma suka kaure da rigima tsakaninsu wanda hakan ya hana shi mayar da hankali ga yin aikin da aka zabe shi. Shekaru takwas da Obasanjo yayi yana mulki shekaru ne da muka yi asararsu a dimukuradiyyance.”

A bayaninsa game da neman afuwar da jam’iyyar PDP tayi kuwa, Prince Momoh cewa yayi, "Neman afuwar dama ai ya zama dole a gare su, amma bayan neman afuwa ai ya zama tilas su dawo da kudaden da suka yi sama da fadi da su, domin idan barawo ya bayar da hakuri kuma bai dawo da kayan da ya sata ba, ai kaga wannan shi ne, Baba na daka gemu na waje kenan."

Da yake amsa tambaya dangane da batun sake tsayawar takarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari kuwa cewa yayi, shi baiga wani abin damuwa a cikin wannan batu ba, domin yan Najeriya ne suke da kuri’unsu a hannu duk wanda ya damu sai yaje yace karda su zabe shi. Kuma tsayawa takara ba fa zarcewa ba ne, mai yasa duk zasu tashi hankalinsu.

Wani abu da yakamata mutane suke duba shi ne ba wai kawai abubuwanda Buhari ya kai ga samun nasarar aiwatarwa zasu na dubawa ba; a’a suna la’akari da cewa shin da ba Buharin bane da yanzu mai zai faru?

Maganar da ake yanzu Boko Haram ba ta rike da ko karamin sashe a Najeriya, amma da fa, har Abuja ma suka fara kaiwa hari, kaga wannan ai babbar nasara ce. Ga kuma bangaren aikin gona da jajircewa wajen fitar da kasar nan daga matsin tattalin arziki. Prince momoh ya jaddada.

Kana ya cigaba da cewa, bayan Buhari ya hau ne fa, duk a cikin shekaru uku ne kacal, karfin wutar lantarkin da muke samarwa ya kai har 7,000mw daga 3,000mw da ya gada. Ya kaddamar da tsarin asusun bai daya (TSA) da lambar tsaro ta banki (BVN).

Kuma maganar da Obasanjo yake na cewa Buhari bai cancanta ya a kara zabarsa ba, wannan ra'ayinsa ne kawai, domin ba shi da wani hurumi da zai hana wani tsayawa takara saboda kundin tsarin mulki ya bashi dama.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel