Ta bayyana karara yadda aka kashe Zainab Alizee da diyar ta

Ta bayyana karara yadda aka kashe Zainab Alizee da diyar ta

Sabbin dalilai a ranar Alhamis ta yau sun bayyana dangane da yadda dan kasar Denmark, Peter Nielsen, ya kashe shahararriyar mawakiya Zainab Alizee tare da diyar ta 'yar shekaru 3, Petra, a gidan su na Banana Island dake birnin Ikoyi na jihar Legas.

Peter Nielsen wanda shine mijin shahararriyar mawakiyar tuni ya shiga hannu hukuma inda ta gurfanar da shi har gaban kuliya manta sabo.

Tun a ranar Larabar da ta gabata ne Effiong Asuquo, babban jami'in 'yan sanda ya shaidawa kotun Majistire ta garin Yaba a jihar Legas cewa, wanda ake tuhuma ya rinka gwara kan matar sa a bango da har ya kai ga mutuwar ta, kana ya diddikawa diyar su guba.

Ta bayyana karara yadda aka kashe Zainab Alizee da diyar ta
Ta bayyana karara yadda aka kashe Zainab Alizee da diyar ta

Mista Asuquo dai ya tabbatar wa da kotun cewa, Peter Nielsen shine ya kashe Zainab da kuma diyar ta a ranar Larabar da ta gabata a cikin gidan su mai lamba 17 dake unguwar Banana Island ta birnin Ikoyi.

Legit.ng da sanadin shafin jaridar Premium Times ta fahimci cewa, wannan laifi ya sabawa sashe na 223 cikin dokokin jihar ta Legas kuma babu hukunci da ya dace face na kisa. Sai dai alkalin kotun ya daga sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Mayu domin neman shawarar magabatan sa ta fuskar shari'a.

KARANTA KUMA: Wata Mata ta gurfana gaban Kuliya da laifin sace jaririya 'yar watanni 7 da haihuwa

A fari Peter Nielsen ya ki amincewa da aikata laifi, inda ya ce ya farka daga bacci kuma ya yi kacibus da gawar iyalan sa a dakin girki wanda ta yiwu sun mutu ne sakamakon shakar iskar gas.

A yayin haka kuma, wata jarumar fina-finai na dandalin Nollywood, Omoni Oboli, ta yi kira kan a tabbatar da adalci bisa ga mutuwar mawakiya Alizee.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng