Operation Lafiya Dole: Sojoji sun tarwatsa Boko Haram, sun kuma ceto mutane (hotuna)

Operation Lafiya Dole: Sojoji sun tarwatsa Boko Haram, sun kuma ceto mutane (hotuna)

- Sojojin Operation Lafiya Dole sun cigaba da wargaza Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas

- Sojojin sunyi nasarar kashe uku daga cikin ‘yan Boko Haram a jihar Borno

- Sun kuma yi nasarar cewo mutane 33 na iyalan ‘yan Boko Haram

Sojojin 28 Brigade masu aikin Operation Lafiya Dole a ranar Laraba 11 ga watan Afirilu, tare da mafarauta da ‘yan banga na jihar Borno sukayi artabo da wasu ‘yan Boko Haram.

Legit.ng ta ruwaito cewa Daraktan Sojojin na harkokin jama’a Burgediya janar Texas Chukwu, yace sunyi nasarar kashe uku daga cikin ‘yan Boko Haram din, a lokacin da ake musayar wuta a tsakanin sojojin da ‘yan Boko Haram.

Operation Lafiya Dole: Sojoji sun tarwatsa Boko Haram, sun kuma ceto mutane (hotuna)
Operation Lafiya Dole: Sojoji sun tarwatsa Boko Haram, sun kuma ceto mutane

Sojojin sun kuma yi nasarar cewo mutane 33 na iyalan ‘yan Boko Haram. Wadanda aka ceto din sun hada da Mata 15, sai yara maza 6, sai ‘yan mata 12. Kuma gidajensu da kayayyakinsu an lalatasu an kona.

Operation Lafiya Dole: Sojoji sun tarwatsa Boko Haram, sun kuma ceto mutane (hotuna)
Operation Lafiya Dole: Sojoji sun tarwatsa Boko Haram, sun kuma ceto mutane

KU KARANTA KUMA: Bukar yayi kokarin samun amincewar majalissa akan gina Poly ta tarayya a jihar Katsina kafin rasuwarsa - Sanatoci

Bayan haka a kalla mutane 95 daga cikin ‘yan Boko Haram wadanda aka kama a shekarun baya a shirye suke da komawa cikin jama’a don cigaba da rayuwa kamar kowa, bayan basu kula da horo da kuma

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng