An biya kowannenmu N5m domin tsige Na’Abba – Jagaba ga kotu
Jami’in tsohon shugaban kasa Olushegun Obasanjo, ya biya mambobin majalisar wakilai N500, kowannensu domin su tsige tsohon kakakin majalisa, Ghali Umar Na’Abba.
Shugaban kwamitin harkokin cikin gida na majalisar, Hon. Jagaba Adams Jagaba ne ya bayyanan akan a jiya yayinda yake bayar da shaida a gaban wani kotun tarayya dake Lugbe a shari’ar Hon. Farouk Lawan da ake yi bayan an zarge shi da cin hanci a lokacin tallafin kudin mai.
Da yake amsa tambayoyi daga lauyan Lawan, Mike Ozekhome (SAN), Jagaba ya fadama kotu cewan jami’in gwamnati ne ya kawo kudin domin toshiyar bakin mambobin majalisar dokoki musamman domin a tsige kakakin majalisa a wannan lokaci, Na’Abba.
KU KARANTA KUMA: 'Danyen man da ake hakowa a Najeriya kowace rana ya ragu da ganga 82, 000
Yace ya kai rahoton lamarin ga majalisa a lokacin zaman majalisa sannan kuma ya bayyana kudin.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng