Wani Mutum ya saki matarsa bayan tayi yunkurin kashe kanta

Wani Mutum ya saki matarsa bayan tayi yunkurin kashe kanta

- Ina rokon kotu da ta raba aure na da wannan matar a cewar wani magidanci

- Matar tawa ba ta jin magana, tana da wuyar sha’ani

- Alkalin kotun ya kuma bashi hadin kai, ya sakar masa matar amma sai dai ya umarci da ya biya ta wasu kudade

Wata kutu dake garin Agodi na jihar Oyo, ta raba auren wasu ma’aurata bayan sun shafe shekaru biyar da aure.

Ma’auratan da aka bayyana sunansu da Selim Osuntade da matarsa Mutiat, mijin matar ya gamsar da kotin yunkurin matar na kashe kanta.

Alkalin kotun mai shari’a Chief Mukaila Balogun, yace kotun ta gamsu da korafin mai karar, sannan ta amince da ta raba auren.

Wani Mutum ya saki matar bayan tayi yunkurin kashe kanta

Wani Mutum ya saki matar bayan tayi yunkurin kashe kanta
Source: UGC

KU KARANTA: Wata Mata ta gurfana gaban Kuliya da laifin sace jaririya 'yar watanni 7 da haihuwa

Mijin matar yace yayi duk mai yiwuwa wajen fadakar da matar tasa, sakamakon bata jin magana, amma da yake kunnen kasha gare taki ji.

Yace: “Har daina mu’amalar aure nayi da itako ta tuba ta dai mugun halin nata amma tayi biris taki dainawa.”

Matar mai karar dai ta amince da laifinta na rashinji amma bata amsa laifin yunkurin kashe kan nata ba, sai dai ta roki kutun da ta sulhunta su.

Mijin matar Selim Osuntade ya kekasa kasa yace ina a kai kasuwa, domin tabbas da ta kasha kan nata da wahalar da zai shiga ba wanda yasan karshenta.

Daga karshe mai shari’a Balogun, bayan raba auren ya umarci mijin nata da ya biya ta Naira dubu N5000 da zata dauko hayar motar da zata kwashwe komatsanta, da Naira dubu N12,000 kudin hayar da zata kama wani daki haya da karin wata Naira dubu N8,000 duk wata domin kula da yayansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel