Tazarcen Buhari: Zai kai labari kuwa? Sharhin marubuci
Babu tantama a 'yan siyasar duniya masu farin jini a yau, shugaba Muhammadu Buhari na daya cikin ukku, A zamanin nan, irin soyayyar da ake yi masa, in da a da ne, sai abn ya zamo wani sabon addini ko darika, arewar Najeriya na son danta.
Tun bayan da ya ayyana niyyarsa ta sake tsayawa takara, lissafin ya canza a siyasar kasar nan, inda jam'iyyu suka tabbtar cewa a babban zabe, dashi zasu kara, masu jiran ya hakura kuwa, suka lakume mayatarsu.
Babu tantama a 'yan siyasar duniya masu farin jini a yau, shugaba Muhammadu Buhari na daya cikin ukku, A zamanin nan, irin soyayyar da ake yi masa, in da a da ne, sai abn ya zamo wani sabon addini ko darika, arewar Najeriya na son danta.
Shugaban, yana da mabiya, masu ilimin akwai, masu kudin akwai, makaffin masoyan yana dasu, kuma haka ma yana da mahassada na gani kashe ni, daga bangarorin kasar nan da dama.
Shi dai shugaba Buhari akwai kyakkyawar niyya, kuma da gaskiya, baya sata, baya cuwa-cuwa, baya karya ba kuma ya yaudara da aka san 'yan siyasa da ita, wadannan alamu ne na gobensa ta 2019 zata yi armashi.
DUBA WANNAN: Yawan 'yan najeriya a yau
Matsalolin dai da zai fuskanta sune, bakin talauci, rashin hakurin 'yan Najeriya, cikas din da tattalin arziki ya samu a baya, tsaro, yawan masu jira a basu, Boko Haram, tarin almajirai da bassu da iyaye da ya kamata ya ceta, da ma kuma tsufa da tattalin lafiya.
Shugaban ya samar da aikin yi, amma abin da yawa. Ya kawo jari, amma kadan suka samu. Ya kama barayi amma lauyoyi sun makale ceton kudin. Ya dawo da martabar noma. Ya ci uban Boko Haram har ta gudu jeji. Ya samar da alkibla ga tattlin arziki.
Kura kuransa sun hada da, rashin sauri, rashin fahimtar yadda zamani yake da tafiyar da tattalin arziki. Romon baka daga wadanda suka zagaye shi, kila-wa-kala kan lafiyrsa, da ma zargin wasu na arzurta kansu a gwamnatinsa.
Wadannan sune abubuwa da zasu taimaki, ko tadiye kaar shugaba Buhari a 2019.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng