Dubu ta cika: Hukumar NAPTIP ta damke masu safarar mutane 8
- Asirin wasu masu fataucin mutane ya toni, bayanda humaka tayi ram da su
- An bukaci mutane da su nesata kansu da wannan mummunar sana'ar domin gwamnati ba zata saurarawa duk wanda ta kama ba
Babban kwamandan hukumar dake yaki da masu fataucin mutane (NAPTIP) na jihar Benin, tayi damke wasu wadanda ake zargin masu fataucin mutane ne har su twakwas.
Kwamandan NAPTIP na jihar Mr. Nduka Nwanwennne ta shaida hakan ne ga manema labarai a yau Laraba, inda tace, an kame wadanda ake zargin ne tun bayan watnni uku da suka gabata.
Tace, hukamar tasu tayi nasarar kubuto da mutane har 138 a ckin watanni ukun, kuma har sun sada 124 da iyalansu daga cikin wadanda suka ceton.
KU KARANTA: Labari mai dadi: Masu hasashe sunce tattalin arzikin Najeriya yanata kara habaka
Nwanwanne ta cigaba da cewa, a yanzu haka suna shari'o'i har 89 a kutuna daban-daban da ba kammala yanke hukunci ba, kuma 34 daga cikinsu mutane ne su kayi korafi yayinda 14 kuma abokan aikinsu jami'an tsaro ne suka kawo musu.
Shugaban hukamar ta bayyana takaicinta dangane da yadda har yanzu ake cigaba da samun masu kunnne kashin da suke cigaba da shiga wannan mummunar sana'a ta safarar mutane, duk kuwa da cewa gwamnati da masarautun gargajiya na ɗaukar matakai masu tsauri akan duk wanda aka kama.
A cewarta, gwamnatin jihar ta Edo ta kara matsa kaimi wajen cigaba da wayar da kan mutane illar dake tattare da wannan mummunar sana'ar.
Daga karshe, Nwanwenne ta yabawa basaraken yankin Oba Ewuare, bisa namijin kokarin da yake na dakile masu fataucin mutane a yankin. Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng