Labari mai dadi: Masu hasashe sunce tattalin arzikin Najeriya yanata kara habaka

Labari mai dadi: Masu hasashe sunce tattalin arzikin Najeriya yanata kara habaka

- Hukumar Kididdigar tattalin arziki tayi kididdigar wata-wata tace tattalin arzikin Najeriya yana ta kara habaka ta fannin kasuwanci

- Hukumar kididdigar ta FSDH nasa ran cewa arzikin kasar zai koma 13.49% a cikin watan Maris

- FSDH ta bayyana cewa Ofishin kula da bashi na kasa (DMO) yana aiki game da hanyoyin da za’a bi don rage bashin gwamnatin tarayya

Hukumar Kididdigar tattalin arziki ta FSDH, tayi kididdigar wata-wata tace tattalin arzikin Najeriya yana ta kara habaka ta fannin kasuwanci, a rahoton data bayar a watan Maris 2018, cewa arzikin kasar zai koma 13.49%.

FSDH ta bayyana cewa Ofishin kula da bashi na kasa (DMO) yana aiki game da hanyoyin da za’a bi don rage bashin gwamnatin tarayya.

Labari mai dadi: Masu hasashe sunce tattalin arzikin Najeriya yanata kara habaka
Labari mai dadi: Masu hasashe sunce tattalin arzikin Najeriya yanata kara habaka

"Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa zata daga bashi mafi karanci a kwata na farko cikin shekarar 2018. Wannan cigaba zai kara tallafawa ajiyar gwamnatin tarayya na tsaron laluri. Duk da cewa hukumar tana tsammanin samun cigaba daga matsayin da yake.

KU KARANTA KUMA: Tafiyan Landan: Dalilin da yasa Buhari bai rubuta wasika ga majalisar dokoki ba

“Muna sa ran cewa kasuwannin da suka dace sun fahimci kwata na biyu a shekarar 2018, dangane da aikin tarihi. Masu zuba hannun jari zasu iya daukar matakin da ya dace don samun riba a kasuwanci”, inji shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel