Nigerian news All categories All tags
Gado girman da: Babban dan Adam A. Zango ya fitar da zazzafan kundin wakokin Hip Hop

Gado girman da: Babban dan Adam A. Zango ya fitar da zazzafan kundin wakokin Hip Hop

- Babban dan Adam A. Zango ya fitar da zazzafan kundin wakokin Hip Hop

- Kundin wakokin da yaron ya fitar na kunshe ne da wakoki uku

- Haidar din ya taba fitowa a wani fim wanda yayi suna sosai

Kamar dai yadda muka samu, babban da ga fitaccen jarumin nan na wasannin fina-finan Hausa kuma mawaki watau Adam A. Zango mai suna Haidar Adam ya fitar da kundin wakokin sa na farko mai suna 'Take Over'.

Gado girman da: Babban dan Adam A. Zango ya fitar da zazzafan kundin wakokin Hip Hop

Gado girman da: Babban dan Adam A. Zango ya fitar da zazzafan kundin wakokin Hip Hop

KU KARANTA: Aina'u Ade ta ayyana lokacin auren ta

Mun dai samu cewa kundin wakokin da yaron ya fitar na kunshe ne da wakoki uku da suka hada da 'Godiya', 'Rayuwa' da kuma 'Taken Over'.

Legit.ng ta samu haka zalika cewa yaron wanda ake yi wa lakani da sunan 'Star Boy' a 'yan kwanakin nan ne da suka wuce ya cika shekaru 11 kacal a duniya.

Haka ma kuma mun samu cewa wakokin da aka saki a kundin na kunshe ne da Engausa watau turanci da Hausa.

Mai karatu ma dai zai iya tuna cewa a shekarun da suka gabata ma dai Haidar din ya taba fitowa a wani fim wanda yayi suna sosai a wancan lokacin mai suna 'Ummi'.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel