Da mamaki: Amaechi ya fadi albashin da ministocin Buhari ke kwasa a duk wata
Babban minista a ma'aikatar sufuri na gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Mista Rotimi Amaechi ya ayyana cewa shi da sauran ministocin Buhari suna karbar Naira dubu 950 ne kacal duk wata a matsayin albashi.
Mista Amaechi yayi wannan ikirarin ne a yayin da yake jawabin sa a wajen wani taron kaddamar da littafin da wani tsohon jami'in gwamnatin tarayya daga jihar ta sa marigayi Dakta Matthew Mbu, tsohon ministan harkokin wajen Najeriya ya wallafa mai taken 'Diginity In Service'.
KU KARANTA: Kotu a Abuja ta kunyata Sifeto Janar na 'yan sanda
Legit.ng ta samu cewa Minista Amaechi dake zaman daya daga cikin jiga-jigan gwamnatin nan ta Buhari ya kuma kara da cewa a cikin kudaden nan ne yake fitar da kudin hayar gida na Naira dubu 350 kuma yake biyan masu yi masa hidima.
A wani labarin kuma, Fadar shugaban kasar Najeriya ta tabbatar da labarin cewa wasu 'yan Najeriya mazauna kasar Birtaniya sun soma yi wa shugaba Muhammadu Buhari zanga-zanga suna bukatar ya janye kudurin sa na sake tsayawa takarar da ya ayyana a zaben 2019 mai zuwa.
Sai dai daya daga cikin hadiman na shugaban kasa ya bayyana cewa wannan ba abunda yake nunawa sai tabbacin cewa shugaban kasar na kokarin dora kasar bisa turbar da ta dace ne shiyasa hakan ke ta faruwa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng