Abubuwa 7 da ka iya kayar da shugaba Buhari a 2019

Abubuwa 7 da ka iya kayar da shugaba Buhari a 2019

Yayinda shugaban kasa ya alanta niyyar sake takararsa a zaben badi kuma domin bada daman muhawara da ilimantar da al’umma, jaridar Legit.ng ta kawo jerin abubuwa 7 da ka iya kayar da shugaba Buhari a 2019.

1. Rikicin makiyaya da manoma

Yayinda aka fara murnar samun nasara a kan Boko Haram, wani sabon rikici ya barke a yankin Arewa maso tsakiyan Najeriya da Arewa maso gabashin Najeriya na rikici da kashe-kashe tsakanin makiyaya da manoma.

Wannan annoba ya yi sanadiyar hallakan rayukan jama’a akalla 1000 zuwa yanzu. Yayinda wasu ke cewa shugaba Buhari ya ki kawar da abun saboda shi Bafulatani ne, wasu sunce da hadin bakin jami’an soji makiyaya da manoma suke kashe jama’a.

Mutane da dama sun hallaka a jihar Benuwe, Taraba, Kogi, Neja, Nasarawa, Plateau, da jihar Adamawa.

2. Tsadar rayuwa

Jama’a sun ce tun da shugaba Buhari yah au mulki a 2015, tsadar rayuwa ya karu. Farashin kayayyakin sun karu. Farashin mai ya tashi daga N87 zuwa N145 ga lita, farashin kayan masarufi sunyi tashin gwauron zabo, yunwa ya karu, kuma mutane sun sha wahala.

3. Rashin tsaro

Da dama sunce ba bu banbancin tsakanin lokacin Buhari da Jonathan a bangaren tsaro saboda kulli yaumin sai an waye gari an yi garkuwa da mutane, fashi da makami, kisa ba gaira ba dalili, jami’an SARS suna hallaka jama’a maimakon karesu, masu kora shanu a jihar Zamfara suna hallaka jama’a da sauransu.

KU KARANTA: Abubuwa 8 da ka iya baiwa shugaba Buhari nasara a 2019

4. Kabilanci da banbancin addini

Siyasar kabilanci da banbancin bai kare a Najeriya ba. Yayinda kungiyar Kiristocin Najeriya CAN ta fito karara ta nuna rashin amincewarta da wannan gwamnati. Kana ta caccaki wasu mabiya addinin da suka kawowa shugaba Buhari ziyara kuma suka nuna masa goyon baya

5. Rikicin jam’iyyar APC

Rabuwar kai da barakar da ke cikin jam’iyyar APC ka iya zama babban cikas ga shugaba Buhari a zabe mai zuwa. Akwai babban rikicin cikin gida tsakanin ‘yayan jam’iyyar.

6. Rashin aikin yi

Game da cewar cibiyar lissafin Najeriya wato National Bureau od Statistics, rashin aikin yi cikin matasa ya karu da kasha 18 cikin 100 cikin shekarun kusa.

7. Adawar Obasanjo, Babangida, Buba Galadima da wasu yan adawan boye

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng