Murna baki har kunne: An kusa fara samun wutar lantarki 24h

Murna baki har kunne: An kusa fara samun wutar lantarki 24h

- Mafarkin samar da wutar lantarki kullum ba katsewa ya dauko hanyar tabbata

Ministan Makamashi, aiyuka da gidaje Babatunde Fashola, yace an samu nasarar canza tsoffin rumbunan samar da wutar lantarki na garin Umuahia da Aba dake karamar tashar samar da wutar lantarki ga jihar Abia da kewaye.

Murna baki har kunne: An kusa fara samun wutar lantarki 24h
Babatunde Fashola

Da yake jawabi, a yayin kaddamar da sabbin na’urorin masu karfin 40MVA 132/33KVA a garin na Umuahia, a jiya Litinin yace, wannan wani yunkuri ne da gwamnantin tarayya take yi da zai habaka tattalin arziki da kuma kawo cigaba ga rayuwar jama’a.

Mutukar al’umma zasu yawaita, to tabbas suna bukatar karin wutar lantarkin, don haka ne Ministan yace, wannan sauyi da akai zai habaka samuwar hasken lantarki a garin na Umuahia da ma wani sashe na jihar Imo.

“Sanin kowa ne samun wuta a kasar nan ya karu, domin a yanzu yakai 7000 MW amma kuma rarraba shi ne aiki. Har yanzu ke zama matsala, sakamakon akwai kimanin 2000 MW da ba’a iya rarraba shi ga masu bukata. Wannan shi yake nuni da cewa, muna da aiki a gabanmu na fadada yadda za’a ke rarraba wutar lantarkin.” Ministan ya fada.

KU KARANTA: Rundunar Sojojin Najeriya sun yi wa ‘Yan Boko Haram lugaden wuta

Fashola yace, kamfanin rarraba wutar lantarki ne na kasa ya sanya sababbin rumbunan wutar (power transformers), inda aka canza tsohuwar na’urar mai karfin 80MVA da sabuwa mai karfin 120MVA, kuma hakan zai kara yawan adadin wutar da yankin yake samu daga 147.5MVA zuwa 227.5MVA.

“Dalilin zuwanmu nan shi ne domin zantawa don fuskantar irin matsalolin da a’ummar wannan yanki suke fuskanta, dagane da wutar lantarki, sai mu san irin yadda zamu nemo mafita.” A cewar Fashola.

Da yake jawabi gwamnan jihar ta Abia, Okezie Ikpeazu, ya jinjinawa gwamnatin tarayyan bisa namijin kokarinta wurin habaka samar da wutar lantarki a jihar, domin hakan zai taimaka wajen bunkasa walwala da tattalin arzikin a’ummar jihar ta Abia.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng