IBB ba Allah bane, Obasanjo ba Allah bane, babu yadda zasu yi da Buhari – Ministan Buhari

IBB ba Allah bane, Obasanjo ba Allah bane, babu yadda zasu yi da Buhari – Ministan Buhari

Ministan harkokin sadarwar a Najeriya, Adebayo Shittu ya bayyana cewa kada magoya bayan shugaba Buhari su girgiza da maganganun tsofaffin shuwagabannin kasa, Obasanjo da IBB game da takarar Buhari a zabukan 2019.

Minister Shittu yace ai dukkansu babu Allah a cikinsu, don haka basu isa su hana Buhari dawowa ba. Shittu ya bayyana haka ne ga kamfanin dillancin labarum Najeriya a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Mun gaji da gafara Sa: Jami’an hukumar Kwatsam sun yi bore game da sabon Inifam da aka kirkiro musu

A ranar Litinin, 9 ga watan Afrilu ne dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2019, da nufin neman tazarce har zuwa shekarar 2023. Buhari ya bayyana aniyar ne a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.

Sai dai tsofaffin shuwagabannin Najeriya da suka hada da Cif Olusegun Obasanjo, da Ibrahim Badamasi Babangida sun shawarci Buharin da kada ya sake ya tsaya takara a shekarar 2019, saboda a cewarsu ya gaza.

Da yake mayar da martani ga IBB da Obasanjo yace: “Waye Obasanjo? OBJ ba Allah bane, IBB ba Allah bane, a zamaninsa, Obasanjo so yayi ya sake tsayawa takara karo na uku, kuma bai samu ba. Kuma ina tabbatar muku sai Buhari ya zarce da ikon Allah.”

Daga karshe Shittu ya bayyana ayyukan cigaba da Buhari ya yi a shekarun ukunsa da suka hada da samar ma matasa 200,000 aikin N-Power, sa’annan wasu guda 300,000 na jira, kashe naira biliyan 255 a fannin sufuri, gidaje da ayyuka, sai kuma aikin titin jirgin kasa da gyaran manyan hanyoyi 25 a Najeriya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng