Iftila’i: Wuta ta kona dakuna 25 da kuma shaguna 12 a Ilorin

Iftila’i: Wuta ta kona dakuna 25 da kuma shaguna 12 a Ilorin

- Wata mahaukaciya gobara ta lankwame gida da shaguna cike da kaya

- Gobarar dai ta fara ci ne tun tsakar dare amma sai wajen asuba ta mutu

- Yanzu haka dai da mazauna da masu sana'a a shagunan gidan duk sunyi tagumi sakamakon babu abinda ya ragu

Kimanin dakuna 25 da kuma karin wasu shaguna 12 makare da kaya ne, suka kone kurmus a sakamakon wata mummunar gobara da ta afku a yankin Kankantu dake Ilorin ta gabas a jihar Kwara.

Iftila’i: Wuta ta kona dakuna 25 da kuma shaguna 12 a Ilorin
Iftila’i: Wuta ta kona dakuna 25 da kuma shaguna 12 a Ilorin

Wani da abin ya faru a idonsa, ya shaidawa wakilinmu cewa, gobarar ta tashi ne a jiya Litinin da wajen karfe biyu na dare (2pm), kuma wutar sai da ta shafe kimanin awanni hudu tana ci, wanda hakan yayi sandiyyar salwantar dukuyoyi masu yawan gaske na miliyoyin Naira. Sannan kuma ta kone dakunan mazauna gidan, wanda yanzu haka ba su da matsugunni.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun damke wani dan fashi daya kware ta hanyar amfani da Keke Napep

Abin mamakin shi ne yadda har yanzu ba wanda ya iya fadar, musabbabin tashin gobarar, daga mazauna gidan da masu haya a shagunan, duk sun ce ba su san yadda akai wutar ta kama ba.

Guda daga cikin wanda gobarar ta shafa, Kale Yero, yace, wani direban tanka ne da yazo wucewa ya ankarar da mutane wutar da ta kama.

Yero ya cigaba dacewa, sai da ma’aikatan kasha gobara na Jihar suka shafe kusan awanni hudu kafin daga bisani su samu nasarar kasha wutar.

Shugaban hukumar kasha gobara ta Jihar Alhaji AbdulWaheed Yakub, ya fadawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN), cewa, watakila wutar lantarki ce tayi sanadiyyar tashin gobarar, kuma tabbas tayi barna sosai kasancewar shagunan makare suke da kaya, amma ba samu rahon rasa rai a gobarar ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel