Abubuwan da suka kewaye shugaba Buhari

Abubuwan da suka kewaye shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa tarihi a siyasar Najeriya, saboda shine mutum na farko daga jam’iyyar adawa da ya doke shugaban kasa mai ci ta hanyar kada kuri’a.

Sai dai tun bayan zaben shugaban kasar ya gamu da cece-kuce game da dama.

Matsalar tattalin arziki na daga cikin manyan kalubalen da suka kewaye gwamnatin Buhari, abun da ya janyo ma sa caccaka daga al’ummar kasar musamman yan adawan shi.

Abubuwan da suka kewaye shugaba Buhari
Abubuwan da suka kewaye shugaba Buhari

Sannan matsalolin tsaro wanda suka hada da tada kayar baya na yan ta'addan Boko Haram, rikicin makiyaya da manoma da dai sauransu.

Haka zalika yaki da rashawa na daga cikin matsalolin da yake fuskanta domin wasu na ganin akwai son kai cewa yan adawa kawai ake yiwa bita da kulli.

KU KARANTA KUMA: Buhari 2019: Cigaba ne mai kyau - Shagari

A ranar Litinin, 9 ga watan Afrilu ne shugaba Buhari ya bayyana kudirisa na sake takara a zaben 2019.

KU KARANTA KUMA: Rabon kwaɗo baya hawa sama: Buhari ya naɗa wasu mutane 26 muhimman mukamai

A halin da ake ciki, Aminu Shagari mamban majalissar wakilai (APC-Sokoto), a ranar 9 ga watan Afirilu ya bayyanawa Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, a birnin tarayya, cewar kudirin Buhari na sake tsayawa takara a 2019 cigaba ne wanda jam’iyyar APC ta samu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel