Sunan da na fi son ake kiran mahaifina da shi - Diyar shugaba Buhari, Zarah Indimi

Sunan da na fi son ake kiran mahaifina da shi - Diyar shugaba Buhari, Zarah Indimi

- Zahra Indimi, diyar shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta bayyana cewa ita ta fi son kiran mahaifinta da lakabinsa na soji wato "Janar"

- Zahra ta bayyana haka ne a wani sharhi da tayi karkashin hoton shugaban kasa da wani mai suna Bayo Omoboriowo, ya saka a shafinsa na zumunta

- Koda wasu suka zo bayyana nasu ra'ayin kan abinda tace, da yawa daga cikin masu sharhin, sun nuna amincewar su cewa sun fi son kiran shugaban kasar da GMB

Zahra Indimi, y'ar gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta bayyana cewa ita ta fi son kiran mahaifinta da lakabinsa na soji "General" fiye da lakabinsa na yanzu wato shugaban kasa "president".

Sunan da na fi son ake kiran mahaifina da shi - Diyar shugaba Buhari, Zarah Indimi
Zahra

Zahra ta bayyana haka ne a wani sharhi da tayi karkashin hoton shugaban kasa da wani mai suna Bayo Omoboriowo, ya saka a shafinsa na zumunta. Ya rubuta PMB a saman. Yayin da Zahra ta zo tofa albarkacin bakita kan hoton, Zahra Indimi ta bayyana da cewa: "Har yanzu na fi son GMB".

DUBA WANNAN: Jami'an SARS sun kulle dan kasuwa a bandakin banki saboda ya ki yi masu alheri

Koda wasu suka bayyana nasu ra'ayin kan abinda tace, da yawa daga cikin masu sharhin, sun nuna amincewar su cewa sun fi son kiran shugaban kasar da GMB, yayin da wasu suka ce, ai yanzun Nigeria kasa ce mai bin tafarkin demokradiyya, don haka dole ne a rinka kiran shi da shugaban kasa ba Janar ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng