Sai Buhari yayi 8 sannan ayyukansa zasu kama kasa sosai - Sanata Ahmad Lawan

Sai Buhari yayi 8 sannan ayyukansa zasu kama kasa sosai - Sanata Ahmad Lawan

- Shugaban majalissa Sanata Ahmad Lawan, ya bayyana cewa tsayawar Buhari takara a shekarar 2019 wani cigaba ne da mutane dama keso

- Lawan ya bayyana haka bayan ganawar sirri da shugaba Buhari yayi da kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC

- Mataimakin wadanda aka rinjaya a majalissa dan jam’iyyar PDP yace sake tsayawar shugaba Buhari takarar shugaban kasa zai taimakawa PDP wurin saukin lashe zaben

Shugaban majalissa Sanata Ahmad Lawan, ya bayyana cewa tsayawar Buhari takara a shekarar 2019 wani cigaba ne da mutane dama keso.

Lawan ya bayyanawa jaridar Vanguard a ranar Litinin bayan ganawar sirri da shugaba Buhari yayi da kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC, shugaban majalissar yace zai taimakawa cigaban da Buhari ya kawo da kuma gwamnatin APC.

Sai Buhari yayi 8 sannan ayyukansa zasu kama kasa sosai - Hassan
Sai Buhari yayi 8 sannan ayyukansa zasu kama kasa sosai - Hassan

Lawan yace “Na fada tun a shekarar da ta gabata cewa Buhari bashi da wata dama dole ne ya sake tsayawa takara. Ya wahala wurin kawo cigaba a Najeriya, duk da babu isassun kayan aiki, sakamakon faduwar kudin danyen mai a duniya, amma gwamnatinsa tayi abubuwa da dama da dan abun abunda take dashi”.

KU KARANTA KUMA: Wadanni na kokarin sanya takalman manyan mutane - Adesina

Mataimakin wadanda aka rinjaya a majalissa dan jam’iyyar PDP, Biodun Olujimi, yace sake tsayawar shugaba Buhari takarar shugaban kasa zai taimakawa PDP wurin saukin lashe zaben 2019. Saboda haka muna masa maraba da shigowa cikin masu neman wannan kujera” inji Sanata Olujimi da Sanata Peter Nwaoboshi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng