Dandalin Kannywood: Shigar mata fim na da matukar muhimmanci inji wata sabuwar jaruma
- Shigar mata sana'ar fim na da matukar muhimmanci inji jaruma Maryam Sparkling
- Maryam ta bayyana cewa ko shakka babu ita shigar ta masana'antar ta karu sosai
- An haifi jarumar ne a garin Zaria ta jihar Kaduna inda kuma ta ce ta girma ne a na Zaria
Daya daga cikin fitattun sababbin fuskoki a masana'antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood mai suna Maryar Zaria da ake yi wa lakani da Maryar Sparkling ta bayyana cewa tabbas shigar mata a dama da su a harkar fim tana da matukar muhimmanci.

KU KARANTA: Aina'u Ade ta ayyana lokacin auren ta
A yayin wata fira da tayi da majiyar mu, jaruma Maryam ta bayyana cewa ko shakka babu ita shigar ta masana'antar ta karu da muhimman abubuwa da dama wanda a da da bata shiga ba ba ta san su ba ko kadan.
Legit.ng dai ta samu cewa an haifi jarumar ne a garin Zaria ta jihar Kaduna inda kuma ta ce ta girma ne a na Zaria da kuma jihar Katsina a wani lokaci a cikin rayuwar ta.
Haka zalika jarumar ta labarta cewa tayi karatun Firamare da Sakandare duka a garin na Zaria kafin daga bisani ta je makarantar kimiyya da kere-kere ta garin Bida, jihar Neja inda ta kammala karatun Difuloma.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng