Mutane 7 sun mutu a jihar Filato
- Mutane bakwai sun rasa ransu a daren Lahadin data gabata, bayan da wasu 'yan bindiga suka bude musu wuta a wani wuri da mashaya suke taruwa, a kauyen Nding dake garin Fan a karamar hukumar Barki Ladi dake jihar Filato
Mutane bakwai sun rasa ransu a daren Lahadin data gabata, bayan da wasu 'yan bindiga suka bude musu wuta a wani wuri da mashaya suke taruwa, a kauyen Nding dake garin Fan a karamar hukumar Barki Ladi dake jihar Filato.
DUBA WANNAN: Aikin gadar sama ta jihar Kano shine abinda jama'ar jihar suka fi bukata - Gwamnatin jihar Kano
Jami'in harka da jama'a na hukumar 'yan sandan yankin ASP Tyopev Terna ya tabbatar da mutuwar mutane biyar, yayinda uku ke karbar magani a asibitin Filato. Sai dai kuma jami'in fannin sadarwa na rundunar 'Operation Safe Haven' Manjo Adam Umar, ya ce mutum biyu daga cikin masu jinyar sun mutu a asibitin.
Manjo Umar ya bayyana cewar, sojojin sun samu kiran waya da bayanin inda lamarin ya faru, sai dai kuma kafin suje wurin maharan sun gudu.
Ya ce babban kalubalen da suke fuskanta shine rashin cikakken bayani da kuma dai dai lokacin da wani abu yake faruwa daga wurin mazauna yankin, sannan ya bukaci matasan yankin dasu kafa kungiyoyi da zasu dinga bawa yankin tsaro, wanda kuma zasu dinga taimakawa jami'an tsaro don magance matsalolin dake afkuwa a yankin.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng