Mutane 6 da har cikin zuciyarsu basu ji dadin sake tsayawar Buhari zabe a 2019

Mutane 6 da har cikin zuciyarsu basu ji dadin sake tsayawar Buhari zabe a 2019

- Idan ana jin haushinka ko ruwa ka fada sai a ce ka tayar da kura, balle kuma kayi sukuwa a sahara

- Bayan amincewa da tsayawa takara, Shugaba Buhari ya fice zuwa birinin London in da ya bar Najeriya cikin dumamar yanayin siyasa

- Amma an yi walkiya kuma ta hasko wadanda amincewa ya yi takarae ba ta yiwa dadi ba

A ranar Litinin ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sake tsayawa takara a 2019, ya bayyana hakan ne a yayin taron kwamitin shugabannin jam'iyyar APC a Abuja.

Shugaba Muhammadu Buhari dai yace ya yarda da ya tsaya takarar ne sakamakon yawaitar bukatar hakan daga yan Najeriya.

Kafin dai ya amince zai tsaya takarar, wasu yan Najeriya sun soki aniyar shugaban ta sake tsayawa zaben.

Saboda haka ne Legit.ng ta tattara sunayen mutane 6 da karara suka nuna adawa da batun sake tsayawar Buharin a takara a zaben 2019.

OLUSEGUN OBASANJO

Mutane 6 da har cikin zuciyarsu basu ji dadin sake tsayawar Buhari zabe a 2019
OLUSEGUN OBASANJO

Babu tantamar cewa tsohon shugaban kasar ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen samun nasarar shugaba Buhari a 2015, amma sai dai a baya-bayan nan yana yawaita sukar shugaba Buharin, wanda hatta kai ga ya rubuta masa wasikar da tayi kaurin suna gami da yamutsa hazo, a cikin wasikar ne ya nemi Buharin da ya manta da batun neman takara a 2019 domin bai tabuka abin azo a gani ba.

AYODELE FAYOSE

Mutane 6 da har cikin zuciyarsu basu ji dadin sake tsayawar Buhari zabe a 2019
AYODELE FAYOSE

Ga duk masu bibiyar kakafen sadarwa musamman na zamani (Social Media), ba za su kasa sanin Fayose ba, in dai batun sukar Buhari ne, ta tabba Gwamnan jihar ta Ekiti yana cikin sahun gaba.

KU KARANTA: Siyasa: Mafarkin Ganduje na Baiwa Buhari kuri'a miliyan 5 na shirin zama gaskiya

Ya bayyana Obasanjon da Buhari a matsayin wadanda amfaninsu ya kare a wurin Najeriya, sannan kuma ya bukaci da duk wadanda suka zabi Buharin a shekarar 2015 da su nemi yafiyar ubangiji.

FEMI FANI-KAYODE

Mutane 6 da har cikin zuciyarsu basu ji dadin sake tsayawar Buhari zabe a 2019
FEMI FANI-KAYODE

Tsohon ministan jiragen sama, ya sha yin rubutu iri-iri a jaridu da kafar sadarwa na suka da kushe ga gwamnatin Buhari.

Inda a baya-bayan nan aka ji shi yana cewa, $1b da Buhari ya amince a siyo makamai domin yakar Boko Haram, za'a yi amfani da su ne don yin kamfen Buhari ya kara zarcewa a 2019. Sannan yayi kira ga yan Najeriya da kada su sake zabar Shugaba Muhammadu Buhari.

Mutane 6 da har cikin zuciyarsu basu ji dadin sake tsayawar Buhari zabe a 2019
IBRAHIM BABANGIDA

Duk da dai tsohon shugaban kasar bai kuncewa Buharin zani a kasuwa ba, amma ya ce yan Najeriya da su cigaba da hakuri da Buharin amma da zarar ya gama wa’adin mulkinsa kada a kara zabarsa 2019, a zabi shugabanni matasa sabbin jinni da zasu farfado da martabar kasar nan.

Janar Babangida dai shi ne wanda ya yiwa Buhari juyin mulki a shekarar 1985, sannan yayi mulki har zuwa 1993.

ANGO ABDULLAHI

Mutane 6 da har cikin zuciyarsu basu ji dadin sake tsayawar Buhari zabe a 2019
ANGO ABDULLAHI

Farfesa Ango Abdullahi, kakakin kungiyar dattijan Arewa ya bayyana amincewa da APC tayi na Buharin ya kara tsayawa takara a matsayin wani nau’i na cin-hanci.

Kuma a ranar 24 watan Maris ne, ya jagoranci gungun hadakar kungiyoyin dattijan Arewa da suka fitar da sanarwar sallama Buharin tare da cire tsammanin zai iya, bayan da suka ce ya baiwa yankin na Arewa kunya.

OLUBUNMI OKOGIE

Mutane 6 da har cikin zuciyarsu basu ji dadin sake tsayawar Buhari zabe a 2019
OLUBUNMI OKOGIE

A watan Janairu ne, babban malamin kiristan dan darikar Catholic dake jihar Lagos, ya shawarci Buhari da ya girmama kansa ta hanyar sauka da zarar ya kammala wa'adin farko tun kafin tusa ta kurewa bodari.

A cewar malamin kiristan, "Makin da Buharin ya ci tun bayan darewa shugabancin kasar nan ba wani abin a zo yaba ba ne, a don haka ya shawarce shi da ya sake tunani wajen nemo mafita ga irin matsalolin da yan Najeriya ke fuskanta."

Don a cewarsa, " Mai Buhari yayi ne wai tunda aka zabe shi? Bai yi wani abin a zo a gani ba. A saboda da haka ya taimaki kansa ya sauka idan ya gama a 2019 ba tare da wani kace-nace ba. Yunkurin tsayawa zabe kuwa a 2019 na tamkar rashin godewa wadanda suka zabe shi ne a 2015 da ma sauran yan Najeriya don ya raina musu hankali."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel